Labarai

Yadda aka yi wa wasu ‘yan mata tsirara a hotunan da AI ya kirkira

Yadda aka yi wa wasu 'yan mata tsirara a hotunan da AI ya kirkira

Mazauna wani karamin gari a kudancin Sfaniya sun shiga cikin wani yanayi na kaduwa bayan da aka gano cewa hotunan tsiraicin ‘yan matan yankin da aka yi amfani da AI sun karade shafukan sada zumunta ba tare da saninsu ba.

 

An kirkiro hotunan ne ta hanyar amfani da hotunan ‘yan matan na asali sanye da tufafi, in da dama daga cikinsu sun saka hotunansu a shafinsu na sadazamunta.

APPLY NOW!  Abunda ya Faru Bayan Ansawa Nijar Takunkumi

 

Wata manhaja ce ta sarrafa wadannan hotunan ta fito da tsairaicinsu.

 

Ya zuwa yanzu ‘yan mata fiye da 20 masu shekaru 11 zuwa 17, sun fito fili sun bayyana cewa su na cikin wadanda alamarin ya shafa da ake zargi wani da ke kusa ko cikin garin Almendralejo a kudu maso yammacin lardin Badajoz ya aikata wannan aika-aikar.

APPLY NOW!  Laifin Me Maryam Shatty Tayi Aka Cire ta a minista??

 

“Wata rana ‘yata ta dawo daga makaranta sai ta ce ‘mama akwai wasu hotuna na da ke yawo da suka nuna tsiraici na’,” in ji Maria Blanco Rayo, mahaifiyar ‘yar shekara 14.

 

“Na tambaye ta ko ta dauki hoto tsirara, sai ta ce, A’a mama, wadannan hotunan ‘yan mata na bogi ne da aka kirkiro da yawa ,yanzu haka kuma akwai wasu ‘yan mata a ajinmu da su ma hakan ya faru da su.’

APPLY NOW!  Yan sanda sun kama wani mutum bisa laifin dukan ƴaƴansa har suka mutu

 

Ta ce iyaye mata 28 da alamarin ya shafa sun kafa wata kungiyar taimaka mu su saboda abu ne da zai iya su shiga cikin damuwa.

 

‘Yanzu haka ‘yan sanda na gudanar bincike, kuma rahotanni sun ce, an gano yara maza akalla 11 da ke yankin da hannu a cikin hotunan da aka kirkiro ko yada su ta manhajojin WhatsApp da Telegram.

APPLY NOW!  Alqawura 6 Da Tinubu Ya dauka A jawabansa Na Jiya

 

Masu bincike na kuma duba zargin cewa an yi yunkurin karbar kudi daga hannun daya daga cikin ‘yan matan ta hanyar amfani da hotonta na bogi.

 

Tasirin hotunan da su ka karrade shafukan sada zumunta a kan ‘yan matan ya bambanta. Madam Blanco Rayo ta ce ‘yarta na tafiyar da harkokinta yadda ya kamata, amma wasu ‘yan matan “ ba sa iya barin gidajensu”.

APPLY NOW!  Yadda aka sace mata kimanin Arba'in a Borno

 

Yawan al’ummar Almendralejo ya zarce dubu 30 wanda ya shahara wajan samar da zaitun da jan barasa. Sai dai al’amarin ya ja hankalin jama’a, abinda kuma ya sa garin ya kasance a cikin kanun labaran kasa.

 

Wannan ya biyo bayan kokarin da daya daga cikin iyayen ‘yan matan, Miriam Al Adib ta yi. Likitar mata ce wacce ta yi amfani da shaharar da ta yi a kafofin sada zumunta wajan gabatar da wannan batu a gaban bainar jama’a domin ayi muhawara a kai.

APPLY NOW!  Shugaba Biden na fuskantar barazanar tsigewa

 

Kodayake an yi ammanar cewa yawancin hotunan na AI an kirkirosu ne a lokacin bazara, amma a kwanakin baya baya nan ne alamarin ya bayyana bayan Dr Adib ta wallafa wani hoton bidiyo tana karfafa gwuiwar ‘yan matan da abin da ya shafa da kuma iyayensu.

 

” Ba mu san yara nawa ne suke da hotunan ba, ko an saka su a shafukan batsa – duk mun damu da haka ,” in ji ta .

APPLY NOW!  Gwamnan Zamfara na zargin Gwamnatin Tarraya da ƙoƙarin hada kai da Yan bindiga domin sulhu

 

” A duk lokacin da aka yi maka laifi , alal misali idan aka yi maka sata , za ka shigar da kara a gaban hukuma kuma ba za ka boye ba saboda wani ne ya yi maka laifi . Amma laifukan da suka jibanci cin zarfai ta hanyar lalata ko nuna tsiraici kan sa wanda aka yi wa laifi ya ji kunya tare da buya koma ya dora alhari a kansa. Shi yasa na isar da wannan sako: cewa wannan ba laifinki bane.”

APPLY NOW!  Babban Bankin Najeriya Ya karyata zan zai Canja Kuɗaɗen kasar

 

Wadanda ake tuhuma da laifi samari ne masu shekaru 12 zuwa 14.

 

Dokokin Sfaniya ba su yi wani tanadi ba a kan laifukan da suka shafi hotunan batsa da aka kirkira da suka shafi manya ba, kodayake za a iya daukar hotunan da aka kirkiro ta hanyar amfani da yara a matsayin hotunan batsa.

APPLY NOW!  Ƴan sanda sun kama mutum 20 bisa zargin garkuwa da mutane

 

Wata tuhuma da za a iya amfani da ita, ita ce keta dokokin sirri.

 

A kasar Sfaniya , yara kanana za su iya fuskantar tuhumar aikata laifi ne daga shekara 14 zuwa sama.

 

Al’amarin ya haifar da damuwa tsakanin mazauna wasu yankuna.

 

” Mu da muke da yara mun damu sosai.,” in ji Gema Lorenzo, wata mata mai yara yaro mai shekara 16 da ya mace mai shekara 12 .

APPLY NOW!  Sojojin Nijar sun amince da karban Sojojin Mali da Burkina Faso

 

Francisco Javier Guerra, mai sana’ar fenti ya ce iyayen yaran da abin ya shafa su ne ke da laifi . ” Ya kamata su yi wani abu a baya , kamar duba wayoyinsu ko saka manhajar da ke bibiyar abubuwan da yaransu ke yi da wayoyinsu.”

 

Wannan ba shi ne karon farko da irin wannan lamari ya zama labari a kasar ta Sfaniy ba .

APPLY NOW!  Alqawura 6 Da Tinubu Ya dauka A jawabansa Na Jiya

 

A farkon shekarar da mu ke ciki an wallafa hotunan tsiraicin mawakiya Rosalfa da AI ya kirkiro a shafukan sada zumunta.

 

“Mata daga sassa daban -daban na duniya sun rubuta min wasika suna bayyana cewa hakan ya faru da su kuma ba su san abin da za su yi ba,” in ji Miriam Al Adib.

APPLY NOW!  Abunda ya Faru Bayan Ansawa Nijar Takunkumi

 

“A halin yanzu wannan na faruwa a sassan duniya daban-daban . Bambancn kawai shi ne a cikin Almendralejo mun tayar da jijiyoyin wuya.”

 

Damuwar it ace manhajojin da aka yi amfani da su Almendralejo sun kara zama ruwan dare gama gari.

 

Javier Izquierdo, shugaban sashin kare hakkin yara a sashin yaki da masu aikata laifukan intanet ya fada wa kafafofin yada labarai sfaniya cewa irin wadannan laifukan sun sauyo salo, ba kamar yadda aka saba gani a baya ba inda wani daga mabuyarsa zai shiga intanet domin ya sauke hotunan batsa na yara”.

APPLY NOW!  Ƴan sanda sun kama mutum 20 bisa zargin garkuwa da mutane

 

Ya kara da cewa : ” har yanzu matsalar ba ta sauya zani ba amma sabon kalubalen da ake fuskanta shine damar da yara kananan suke samu wajan amfani da irin wannan fasaha, kamar irin abinda ya faru a cikin irin wannan yanayi.