Yadda aka yi wa wasu ‘yan mata tsirara a hotunan da AI ya kirkira

Mazauna wani karamin gari a kudancin Sfaniya sun shiga cikin wani yanayi na kaduwa bayan da aka gano cewa hotunan tsiraicin ‘yan matan yankin da aka yi amfani da AI sun karade shafukan sada zumunta ba tare da saninsu ba.   An kirkiro hotunan ne ta hanyar amfani da hotunan ‘yan matan na asali sanye … Read more

Wani Bangare na kotun ƙolin Najeriya ya kama da wuta

Wani ɓangare na harabar kotun ƙolin Najeriya da ke birnin Abuja ya kama da wuta a safiyar ranar Litinin.   Shugaban Hukumar agajin gaggawa a Yanklin Birnin Tarayya, Abbas Idris ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin, inda ya ce tuni jami’an kai ɗauki suka isa harabar kotun, sai dai ya tabbatar da cewa lamarin … Read more

Gwamnan Zamfara na zargin Gwamnatin Tarraya da ƙoƙarin hada kai da Yan bindiga domin sulhu

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bukaci gwamnatin tarayya ta gudanar da cikakken bincike game da wata tattaunawar sulhu a boye da ake yi da Yan bindiga a jihar. Rahotanni sun bayyana cewar tawagar wasu hukumomi da Gwamnatin Tarayya ta aika sun fara tattaunawa da kungiyoyi Yan bindiga ba tare da sanin gwamnatin jihar ba. … Read more

Ƴan sanda sun kama wani mutum bisa laifin dukan Yarsa har ta mutu

Ƴan sanda a kasar Thailand sun kama wani magidanci bisa zargin shi da lakaɗa wa Yarsa mace tare da wasu ƙananan ƴaƴansa dukan da ya yi sanadin mutuwar su. Haka nan kuma mutumin, mai suna Songsak Songsaeng ya kashe wasu ƴaƴansa maza ƙanana guda biyu a lokacin da yake tare da wata tsohuwar matarsa. Waɗannan … Read more

Dalibi ya ratsa ƙasashe shida a kan keke don shiga Jami’ar Al-Azhar

Wani ɗalibi ya yi tafiyar kilomita 4,000 a kan keke inda ya keta ƙasashen Afirka ta Yamma, inda ya jurewa kamu da tsananin zafi don samun gurbi a jami’ar da yake buri.   Mamadou Safayou Barry ya tashi ne daga ƙasar Guinea don zuwa mashahuriyar jami’ar Al-Azhar ta ƙasar Masar a watan Mayu, da fatan … Read more

Yadda zai faru idan aka kwace kujeran Gwamna a Kotun Gaba

Idan Shari’ar zabe ba tayi mun dadi ba a matsayina na ‘dan takara me ya kamata nayi bayan Tribunal (Kotun sauraren kararrakin zabe) bata bani gaskiya ba? _________________________ A tsarin dokokin Nigeria idan Kotu tace baka ci zabe ba kana da damar daukaka ‘kara. Amma ina so mu sani, Appeals wato daukaka ‘kara da suke … Read more

Mutane na shan ruwan zafi saboda yunwa a

Al’ummar Najeriya na fama da matsaloli na hauhawar farashi da tsadar rayuwa abin da wasu masu lura da al’amura ke nuna cewa jama’a na bin wasu hanyoyi domin su tsira da rayuwarsu.   Hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS, har ta yi gargaɗi cewa hauhawar farashin kaya tana yin barazana ga tattalin arzikin ƙasar.   Gargaɗin … Read more

Girgizar Kasa Ya Hallaka Dalibai A Morocco

“Na shiga tunanin ina riƙe da rajistar ɗalibai ina jan layi kan sunan ɗalibai ɗaya bayan ɗaya, har sai da na goge sunaye 32; waɗanda duk sun mutu.”   Nesreen Abu ElFadel, malamar da ke koyar da darasin Arabiya da Faransanci a Marrakesh, tana tuna yadda ta ruga zuwa ƙauyen Adaseel da ke kan tsauni … Read more