Labarai

Abin da ya kamata ku ci idan kuna son yin ƙiba

Abin da ya kamata ku ci idan kuna son yin ƙiba

Abin da ya kamata ku ci idan kuna son yin ƙiba

.

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Yayin da mutane da dama suke burin sirancewa, akwai waɗanda suke rayuwa cikin ƙunci saboda rama da rashin ƙiba.

Abinci mai ɗauke da sindarai masu inganci

Ana samun ƙiba ba tare da yawaita shan abubuwan sha masu ɗauke da sukari da sindarai ba, da kuma rungumar ciye-ciyen kayan ƙwalan da maƙulashe.

Farfesa Linda Bobrof ta Jami’ar Florida, ta shaida wa BBC cewar cin abinci sau uku a rana tare da haɗawa da cin kayan ƙwalama ne hanya mafi sauƙi ta samun ƙiba.

.

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Abincin mai ƙunshe da ƴaƴan itatuwa

Farfesa Bobrof ta ƙara da cewar:

Gyaɗa da riɗi da yalo da man kwakwa suna da maiƙo na ƴaƴan itatuwa wanda ke ƙunshe da sanadarai da kitse mai amfani ga jiki.

Muhimmin abu shi ne, zaɓin abinci mai ɗauke da sinadaran gina jiki.

Tara ƙwanji

Dalilan da suke sa wasu mutane su buƙaci ƙiba sun haɗa da sha’awar tara ƙwanji don wasannin motsa jiki da kuma maye gurbin rashin cin abinci da kuma samun siffa irin ta lafiyayyun mutane.

.

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES

Bayanan hoto,Kayan abinci masu gina jiki

”Kuna iya haɗa nama da kifi da shinkafa ko sauran abinci mai sanya kuzari.”

Mutanen da ke yawan motsa jiki kuma ba sa son yin ƙiba, su mayar da hankali ga yawan cin abinci da kayan ƙwalama don samun ƙarin ƙarfin jiki.

Damuwar da marasa ƙiba ke fama da ita

Michelle Salem ƴar wasan ninƙaya a Miami Beach, ta bayyanawa BBC yadda siranta da rashin ƙiba ke hana ta sanya kayan da take so.

A wannan gaɓa, Liliana Carvajal ta faɗi yadda jama’a ke yi mata kallon maras lafiya ko yar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.