Labarai

Ana Shirin Tsige Shugaban Kasar America Joe Biden

Ana Shirin Tsige Shugaban Kasar America Joe Biden

Shugaban Majalisar Wakilan Amurka ya ce Majalisar za ta ƙaddamar da bincike kan batun tsige shugaba Joe Biden a hukumance.

 

Kevin McCarthy ya ce binciken zai mayar da hankali ne kan zarge-zargen “saɓa ƙa’idar aiki, kawo cikas wurin aiki da kuma rashawa.”

 

Ƴan majalisa na jam’iyyar Republican sun kwashe lokaci suna bincike kan Biden tun bayan da suka ƙwace iko da zauren majalisar a watan Janairu.

APPLY NOW!  Shugaban ECOWAS bola Tinubu ya sakawa Nijar Dokoki

 

Ba a dai samu Biden da wani laifi ba takamaimai tun bayan fara bincike-binciken.

 

Wannan ne mataki na farko a tsarin da za a bi wanda zai iya kai ga batun kaɗa ƙuri’a kan tsige shugaban a Majalisar Wakilai ta ƙasar.

 

A wani saƙo da ya fitar a ginin majalisa na Capitol, Mr McCarthy ya ce “akwai ƙwararan hujjoji kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban ƙasar.”

APPLY NOW!  Sojojin Nijar 17 sun hallaka a sakamakon harin ta'addanci

 

Yanzu haka dai ana binciken ɗan shugaban ƙasar, Hunter Biden bisa zargin saɓa wa dokar biyan haraji a harkar kasuwancinsa