Labarai

Ƴan sanda sun kama mutum 20 bisa zargin garkuwa da mutane

Ƴan sanda sun kama mutum 20 bisa zargin garkuwa da mutane

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta ce ta kama wasu mutum 20 bisa zargin yin garkuwa da mutane a faɗin jihar.

 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Usman ya ce, sun kama mutanen ne bayan samun bayanan sirri da samun korafe-korafe wajen jama’a dangane da ayyukan masu garkuwan, da suka addabi sassan jihar.

APPLY NOW!  Wani Bangare na kotun ƙolin Najeriya ya kama da wuta

 

Abdullahi Usman, ya ce duka mutanen sun amsa zargin da ake yi musu.

 

Ya ce jami’ansu suka ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da kuma wata karamar bindiga harba ka ruga.

 

A cewarsa, mutanen da ake zargin sun karɓi sama da naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa daga iyalan waɗanda suka sace wa ƴan uwa.

APPLY NOW!  Abin da ya kamata ku ci idan kuna son yin ƙiba

 

“Rundunar ‘yan sandan ba ta ja da baya ba a ƙoƙarinta na ci gaba da farautar ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka a jihar bisa umarnin babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun,” in ji shi.

 

Usman ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da farautar ‘yan ta’adda a wasu wuraren da suka fi zafafa ayyukansu, musamman ma a Jalingo, babban birnin jihar.

APPLY NOW!  Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi Wa Dakarun Ta Kashedi