Labarai

An Kama Wasu Mata Guda biyu Da Harsasin Bindiga

An Kama Wasu Mata Guda biyu Da Harsasin Bindiga

AN SAN IYAYE MATA DA TAUSAYI

 

Ba shakka an san iyaye mata da tausayi da jin-kai, sai dai kash ba haka abin yake ba a gurin wadannan matan aure guda biyu Rashida Umar da Rukaiya Ladan

 

Jami’an ‘Yan sandan sirri sun kama Rashida da Rukaiya a garin Akwanga dake jihar Nasarawa dauke da harsashin bindiga sama da guda dubu daya

APPLY NOW!  INNÀ LILLAHÍ WA'INNÁ ILAIHÍ RAJI’ÙN: Young Shêikh Yayi Babban Rashi

 

Wadannan matan sun dauko harsashin ne daga wani gari da ake kira Fadan-Karshe dake karamar hukumar Sanga na jihar Kaduna zasu kaiwa ‘yan ta’addan jeji a Kontagora na jihar Niger

 

A tunaninku wani irin kuncin rayuwa ne zai sa wadannan mata shiga wannan mummunan harka na safaran makamai zuwa ga ‘yan ta’adda?

APPLY NOW!  Babban Bankin Najeriya Ya karyata zan zai Canja Kuɗaɗen kasar

 

Talauci?

Yunwa?

Rashin samun kula daga mazajensu?

Rashin tsoron Allah?

 

Yanzu me zasu fadawa mazansu na aure da ‘ya’yansu da iyaye da ‘yan uwansu? Abin akwai tausayi da bacin rai

 

Allah Ya sauwake