Labarai

Wani Bangare na kotun ƙolin Najeriya ya kama da wuta

Wani Bangare na kotun ƙolin Najeriya ya kama da wuta

  1. Wani ɓangare na harabar kotun ƙolin Najeriya da ke birnin Abuja ya kama da wuta a safiyar ranar Litinin.

 

Shugaban Hukumar agajin gaggawa a Yanklin Birnin Tarayya, Abbas Idris ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin, inda ya ce tuni jami’an kai ɗauki suka isa harabar kotun, sai dai ya tabbatar da cewa lamarin ya shafi wani ɓangare ne kawai na kotun.

APPLY NOW!  Shugaba Biden na fuskantar barazanar tsigewa

 

A cewarsa: “ofisoshi biyu ne lamarin ya shafa kuma babu wanda ya rasa ransa.”

 

Abbas ya ƙara da cewa yanzu haka jami’an kai ɗauki sun samu nasarar shawo kan wutar.

 

Bayanan farko-farko da ke fitowa na cewa wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.

Advertisement