Labarai

Wani ɗan ƙaramin jirgi mai saukar angulu ya yi haɗari a Legas

Wani ɗan ƙaramin jirgi mai saukar angulu ya yi haɗari a Legas

Wani ɗan ƙaramin jirgi mai saukar angulu da ya yi haɗari a Legas ya tayar da hankulan mazauna yankin An yi nasarar ceto mutanen da ke ciki da rayukansu duk da kamawa da wutar da jirgin ya yi jim kaɗan bayan faɗuwarsa Hukumomi sun ce haɗarin ya rutsa da ‘yan Najeriya da wasu ‘yan ƙasashen waje, waɗanda yanzu haka ke karɓar kulawa a asibiti.

APPLY NOW!  Gwamnatin Najeriya Za Ta Sake Gurfanar Da Emefiele Kan Wasu Sabbin Tuhume-tuhume

 

tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, ya ce mutanen jirgi mai saukar angulu mai lamba 5N CCQ da yayi haɗari a Oba Akran da ke jihar Legas na nan cikin yanayi mai kyau. Sirika ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter ranar ranar Talata, 1 ga watan Agusta.

 

Hadi Sirika ya miƙa godiyarsa ga Ubangiji, da ya tseratar da rayuwar mutanen da ke cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru.

APPLY NOW!  Allah Ya Yiwa Hajiya Farida Sani Ɗiso Rasùwa, Tsohuwar Matar Sarkin Daura Wacce Akafi Sani Da Giwar Sarkin Daura.

 

Ya kuma roƙi Ubangiji da ya ci gaba da kare rayukan ‘yan Najeriya daga haɗarurruka, sannan kuma ya yi fatan cewa binciken da ake yi zai taimaka wajen kare faruwar hakan a gaba. Ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar mutane su bayar da haɗin kai wajen tsare inda lamarin ya faru domin gudanar da sahihin bincike. An shiga ruɗani, yayin da jirgin sama ya faɗi a Ikeja da ke Legas A baya alfijir.com ta yi rahoto kan haɗarin ƙaramin jirgin sama mai saukar angulu da aka samu a yankin Oba Akran da ke birnin Legas. Da faɗowar jirgin ne ya kama ci da wuta, wanda hakan ya sanya fargaba a cikin mutanen da ke yankin.

APPLY NOW!  Ambaliya ta kashe mutane a Kebbi