Ambaliyar Ruwa: Hukumomi Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum Fiye Da 2,000 A Libya.
Ambaliyar ruwa a kasar Libya hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum 3,000.
Biranen da wannan ambaliyar ta fi shafa sun hada da Derna da Benghazi da Bayda da Al Marj da kuma Soussa.
Guguwar Mediterrenean Daniel ta haifar da mummunar ambaliyar ruwa a Libya wanda ta mamaye unguwanni da rugujewar gidaje a wasu garuruwan da ke gabar teku a gabashin kasar da ke arewacin Afirka. Kimanin mutane 3,000 ne ake fargabar sun mutu, in ji jagoran wata gwamnatin da ta ayyana kanta a gabashin kasar.
Barnar ta bayyana mafi girma a Derna, wani birni a gabashin ƙasar. Har yanzu dai kasar Libya ta rabu tsakanin gwamnatoci biyu masu gaba da juna, daya a gabashi daya kuma a yamma, wanda kowacce ke samun goyon bayan mayakan sa kai da gwamnatocin kasashen waje.
Shugaban kungiyar agaji ta Red Crescent a yankin tun a ranar Litinin ya ce adadin wadanda suka mutu Derna ya kai 150, amma ana sa ran zai karu.
A wata hira ta wayar tarho da ya yi da tashar talabijin ta Almasar jiya litinin, firaminista Osama Hamad na gwamnatin Libyan ta gabacin kasar ya ce ana fargabar mutuwar mutane 2,000 a Derna, kuma ana kyautata zaton bacewar dubbai. Ya ce an ayyana Derna a matsayin yankin bala’i.