Labarai
Sojojin Najeriya sun ceto yar makarantar Chibok bayan shekara 9
Sojojin Najeriya sun ceto ƴar makarantar Chibok bayan shekara 9
Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto daya daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok, wadda mayaƙan Boko Haram suka sace bayan shafe shekaru tara a hannunsu.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa an yi nasarar ceton ne a garin Maiduguri na jihar Borno, kuma an gabatar da ita a hedikwatar rundunar Operation Hadin Kai a ranar Litinin.
Dalibar, wadda ita ce ta hamsin da biyar a jerin ‘yan makarantan da aka sace, ta bayyana cewa mijinta na Boko Haram, ne ya taimaka mata wajen tserewa bayan miƙa wuya ga sojojin Najeriya.
Ta kuma shaida wa gidan talabijin din cewa ta haifi ƴaƴa biyu ga mijinta dan Boko Haram sai dai duk sun rasu.
Kwamandan sojojin, Manjo Janar Gold Chibuisi, ya bayyana cewa an miƙa ɗalibar a asibitin sojoji domin kula da lafiyarta, domin tabbatar da cewa tana cikin ƙoshin lafiya.
Ya ce za a miƙa ta ga gwamnatin jihar domin sada ta da iyalanta.