Labarai
Denmark zata haramta ƙona Alkur’ani Mai Girma

Denmark na shirin haramta ƙona Al-Kur’ani
Ƙasar Denmark na shirin haramta ƙona littafi mai tsarki a dokar kasar, bayan da aka samu faruwar hakan da dama da suka hada da ƙona ƙur’ani, lamarin da ya tunzura musliman ƙasar har suka gudanar da zanga-zangar Lumana.
Harmcin zai shafi duk wasu alamomi da ake amfani da su a addinance da suka hada da gicciya da kiristoci ke amfani da ita Wato plus me nufin Jesus.
Sai dai hakan zai shafi gama garin wurare, za kuma a tabbatar da dokar ta karade dukkan ƙasar nan gaba kadan.
Ministan shari’ar ƙasar ya ce Peter Hummelgaard ya ce dokar zata tabbatar da ƴancin fadin albarkacin baki anma zata Hana cutar da sauran Al’ummar kasa.
Ana sa ran majalisar ƙasar za ta soma mahawara kan dokar cikin wata mai kamawa.