Ƴan sanda sun kama wani mutum bisa laifin dukan Yarsa har ta mutu
Ƴan sanda a kasar Thailand sun kama wani magidanci bisa zargin shi da lakaɗa wa Yarsa mace tare da wasu ƙananan ƴaƴansa dukan da ya yi sanadin mutuwar su.
Haka nan kuma mutumin, mai suna Songsak Songsaeng ya kashe wasu ƴaƴansa maza ƙanana guda biyu a lokacin da yake tare da wata tsohuwar matarsa.
Waɗannan tuhume-tuhume sun biyo bayan gano gawar Yarinyar mai shekara biyu binne cikin ɗakin girki.
Sai dai binciken da ƴan sandan suka gudanar ya gano cewar mutumin yana da lalular tabin hankali Wato cutar ƙwaƙwalwa, ya kuma kashe yaran ne saboda ba ya son koke-kokensu da hayaniya.
An tuhumi matarsa da laifin mutuwar yarsu mai shekaru biyu, yayin da tsohuwar matarsa ke fuskantar tuhumar mutuwar ƴaƴanta maza biyu. Dukkan iyayen uku na tsare a hannun jami`an tsaro.
A farkon wannan wata maƙwaftan Mista Songsak suka sanar da jami`an tsaro a yankin Bang Ken cewar ya na dukan ƴaƴansa mata, rahoton da ya sa ƴan sada suka ceto yaran daga gidan.
Gwajin ƙwayoyin halitta da jami`an tsaro suka gudanar ya tabbatar da Mista Songsak ya kashe wasu ƴaƴansa maza biyu da ya haifa da matarsa ta uku waɗanda aka tono gawarsu shekaru goma da suka wuce, bayan mahaifiyarsu ta shaida wa ƴan sanda yadda ya kashe jarirai hudu.
Ƴan sandan sun tabbatar da ya binne sauran gwawarwakin ne a harabar wani tsohon gidan mai.