Labarai

Nan da shekara ɗaya, za a samu kyakkyawan sauyi a Najeriya – Kashem Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya ce Najeriya za ta samu kyakkyawan sauyi nan da wata tara zuwa shekara ɗaya karkashin mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin ne a ranar Juma’a a birnin St Petersburg yayin wani zama da al’ummar ƴan Najeriya mazauna Rasha.

Kashim ya tabbatarwa ƴan Najeriya musamman ma waɗanda ke zaune a ƙasar Rasha, cewa gwamnatin Tinubu za ta yi aiki tukuru don kawo ci gaba.

APPLY NOW!  Gwamnan ya ba da umarnin raba shinkafa buhu 40,000 don rage radadi

A lokacin da yake tattaunawa da ƴan Najeriya a Rasha, Kashim ya ce “ina tabbatar muku cewa nan da wata tara zuwa shekara ɗaya, za a samu sauyi mai kyau a Najeriya, na faɗi haka ne saboda na yi imani da irin hazakar da Shugaba Bola Tinubu ke da shi.”

Ya ce gwamnati mai ci na yin duk ƙoƙarinta wajen kyautata yanayin tattalin arzikin ƙasar da kuma farafad da kamfanoni da za su kawo mata ci gaba.

APPLY NOW!  Yanda Zaka Samu Amarya A Sauqaqe

Shettima ya kuma suna da burin horas da ƴan Najeriya miliyan ɗaya a ɓangaren ilimin zamani na intanet.