Labarai

Dalibi ya ratsa ƙasashe shida a kan keke don shiga Jami’ar Al-Azhar

Dalibi ya ratsa ƙasashe shida a kan keke don shiga Jami'ar Al-Azhar

Wani ɗalibi ya yi tafiyar kilomita 4,000 a kan keke inda ya keta ƙasashen Afirka ta Yamma, inda ya jurewa kamu da tsananin zafi don samun gurbi a jami’ar da yake buri.

 

Mamadou Safayou Barry ya tashi ne daga ƙasar Guinea don zuwa mashahuriyar jami’ar Al-Azhar ta ƙasar Masar a watan Mayu, da fatan za a ba shi gurbin karatu.

APPLY NOW!  Ambaliya ta kashe mutane a Kebbi

 

Matashin ɗan shekara 25 ya yi tafiyar tsawon wata huɗu ne a kan keke inda ya ratsa ta cikin ƙasashen da ke fama da rikicin ‘yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi da kuma juyin mulki.

 

Ya faɗa wa BBC cewa ya yi farin ciki “matuƙa gaya” da samun tallafin karatu lokacin da ya isa birnin Alƙahira.

APPLY NOW!  Anfani da fetur a Najeriya ya ragu kashi 35 cikin 100

 

Matashin wanda yana da aure har da ɗa ɗaya ya ce ko da yake ba zai iya ɗaukar nauyin karanta Nazarin Addinin Musulunci a Jami’ar Al-Azhar ba, ko kuma ya hau jirgin zuwa ƙasar Masar, shaharar da jami’ar ta yi, ya yi masa ƙaimin cewa bari ya jarraba sa’arsa don yin wannan tafiya mai cike da tarihi.

APPLY NOW!  Farashin dala na ci gaba da sauka a Najeriya

 

Ya dai ratsa ta ƙasashen Mali da Burkina Faso da Togo da Benin da Nijar da kuma Chadi. Al-Azhar na ɗaya daga cikin cibiyoyin nazarin addinin Musulunci mafi tasiri ga mabiya mazabar Sunni a duniya.

 

Kuma tana ɗaya daga cikin jami’o’i mafi tsufa, don kuwa an kafa ta ne a shekara ta AD670. Mamadou Barry ya bar mahaifarsa don zuwa neman ilmin addinin Musulunci, amma dai ya gamu da kallon zargi da kuma ƙiyayya a wasu ƙasashen da ya ratsa ta cikinsu a kan keke.

APPLY NOW!  Masu Tonon Ma'adanai 30 sun Mutu Bayan Ruftawar Kasa

 

A ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, ‘yan ta-da-ƙayar-baya na kai hare-hare a kai a kai kan fararen hula sannan kuma juyin mulkin da aka yi a baya-bayan nan cikin ƙasashen sun janyo rikita-rikitar siyasa.

 

“Tafiya ta cikin waɗannan ƙsashe, tana da wahala saboda ba su da tsaro a wannan lokaci,” in ji Mamadou Barry.

APPLY NOW!  Abunda ya Faru Bayan Ansawa Nijar Takunkumi

 

“Suna da matsaloli sosai kuma mutane a can suna cikin tsoro – a Mali da Burkina Faso mutane sun riƙa kallo na kamar wani mugun mutum. A ko’ina na ga sojoji ɗauke da manyan bindigogi da motoci,” a cewarsa.

 

Ya ce an kama shi kuma an tsare shi har sau uku babu wani dalili – sau biyu a Burkina Faso da kuma sau ɗaya a ƙasar Togo. Sai dai Allah ya tarfa wa garin Mamadou Barry nono lokacin da ya isa ƙasar Chadi.

APPLY NOW!  Yan sandan sun gano mata 26 da ake shirin safara

 

Wani ɗan jarida ya zanta da shi kuma ya buga labarinsa a intanet, abin da ya hankalin wasu masu kyakkyawar niyya har suka ɗauki nauyin biya masa kuɗin jirgi zuwa Masar.

 

Hakan na nufin ya kauce wa shiga Sudan a kan keke, wadda sassanta a yanzu suka koma fagen yaƙi. A ranar 5 ga watan Satumba, ya sauka a birnin Alƙahira.

APPLY NOW!  Wani ɗan ƙaramin jirgi mai saukar angulu ya yi haɗari a Legas

 

Himmarsa ta sanya har shugabar tsangayar nazarin addinin Musulunci, Dr Nahla Elseidy ta gana da shi. Bayan tattaunawa ne kuma, sai ta bai wa Mamadou Barry gurbin karanta fannin addinin Musulunci da cikakken tallafin karatu.