Najeriya da Kanada za su hada kai don

Shugaban Najeriya ya tattauna ta waya da Firaministan Kanada Justine Trudeau, inda suka duba halin da dimokuraɗiyya ke ciki a Afirka.

Shugaban Najeriya ya tattauna ta waya da Firaministan Kanada Justine Trudeau, inda suka duba halin da dimokuraɗiyya ke ciki a Afirka.

A cewar fadar shugaban Najeriya, Bola Tinubu da Mista Trudeau sun amince cewa za su mayar da hankali wajen ƙarfafa mulkin dimokuraɗiyya a Afirka.

“Shugaba Tinubu ya bayyana wa takwaran nasa ra’ayinsa game da halin da ake ciki a Nijar da Gabon,” in ji sanarwar da fadar ta fitar ranar Laraba.

Yayin da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum na Nijar a watan Yuli, irinsu ne dai suka hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo a Gabon a ranar Laraba.

See Also  Yadda zai faru idan aka kwace kujeran Gwamna a Kotun Gaba