
ZAN IYA SADVWA DA MAI HAILA?
ZAN IYA SADVWA DA MAI HAILA? Wannan amsa Kai tsaye shine Haramun ne, anma batun ansa Condo ga Amsar nan 👇
Tambaya:
Salam. Malam Allah ya karama daukaka da imani. Ga tambayata: Shin mutum zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa Condom?
Amsa:
To dan’uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum ko duk wani Nau’in abinda yayi kama da haka saboda Allah ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma yın wanka.
Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za’a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condum .
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
28/11/2015 update on 2023