LabaraiAlfijir Hausa

Yaroń Da Hajiya Layla Ali Othman Ta Ɗauki Nauyinsà Ya Rasú.

Yaroń Da Hajiya Layla Ali Othman Ta Ɗauki Nauyinsà Ya Rasú

 

Yanzu muke samun labarin cewa Allah ya yi wa wannan yaro Khalifa rasuwa sakamakon ciwon da ke damunsa ya ci jikińsa.

 

Jikinsa ya kara tsananta nè a jiya.

 

Khalifa dai shine yaron nan da Layla Ali Othman ta dauki nauyi kula da shi sakamako watsi da shi da mahaifiyarsa ta yi kan cewa alhanine shi.

 

Za a yi masa Sallar Jana’iza anjima a babbar masallacin kasa wato Central Mosque dake Abuja.