Labarai

’Yar Shekara 72 Ta Rasu A Hatsarin Mota

’Yar Shekara 72 Ta Rasu A Hatsarin Mota

’Yar Shekara 72 Ta Rasu A Hatsarin Mota

Wata tsohuwa mai shekaru 72 da wasu mutum biyu sun rasu a sakamakon hatsarin motar fasinja da wata babbar mota a Legas.

Wata tsohuwa ’yar shekar 72 da wasu mutum biyu sun rasu a sakamakon hatsarin motar fasinja da wata babbar mota a cikin dare a yankin Gbagada da ke Jihar Legas.

Hatsarin ya auku ne wata bas mai daukar mutum 18, cike da fasinja ta kwace a hanyarta ta zuwa Oshodi daga Ojo, inda ta yi karo da wata babbar mota.

 

Hukumar sufuri ta Jihar Legas LASEMA, ta ce, “Maza biyu da mace daya sun rasu nan take, wasu kimanin mutum bakwai kuma su samu raunuka.

“An garzaya da wadanda abin ya ritsa da su Babban Asibitin Gbagada”, inda aka kwantar da wasu daga cikinsu a sashen kula da lafiya ta gaggawa, in ji Babban Sakataren LASEMA Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu.

Ya sanar da haka ne a safiyar Lahadi, inda ya bayyana cewa bayan aukuwar hatsarin da dare ne suka samu kiran gaggawa, inda suka je wurin domin kai dauki.