Labarai

’Yan Ta’adda Sun Kashe Jami’in Kwastam A Yobe

’Yan Ta’adda Sun Kashe Jami’in Kwastam A Yobe

’Yan Ta’adda Sun Kashe Jami’in Kwastam A Yobe

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa ayyukan ‘yan Boko Haram a garin Geidam ya karu a ‘yan kwanakin nan.

Wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kashe wani jami’in kwastam mai suna Usman Gombe a Karamar Hukumar Geidam da ke Jihar Yobe.

Aminiya ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kai farmaki sansanin kwastam din da ke kan titin Maine Soroa, a cikin wasu motoci biyu kirar Volkswagen Golf da Land Rover jeep da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar, inda suka fara harbe-harbe kai-tsaye ba tare da sun fuskanci wata turjiya ba.

 

Bayanai sun ce ’yan ta’addan sun kai harin ne a lokacin da suka tabbatar da cewa jami’an kwastam din sun dawo gida daga aiki.

Wannan dai a cewar wakilinmu shi ne ya sanya ’yan ta’addan suka shammace su, lamarin da ya sa barin wutar da suke musu babu kakkautawa wasu daga cikin jami’an suka rika tserewa domin tsira da rayukansu.

“Abin takaici, an harbe daya daga cikin jami’an, Usman Gombe, a lokacin da yake kokarin haura wata katanga domin neman mafaka,” kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu.

Rahoton ya kara da  cewa, maharan sun kuma kona motar sintiri na kwastam guda, jannareta, da kuma wani bangare na ginin gidajen kwastam din.

“Wannan shi ne karo na biyu da ‘yan Boko Haram ke kashe jami’an kwastam, a watan da ya gabata, wani jami’insu Babalola, da karamin jami’insa, na manta sunansa da ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da shi, suka kashe shi,” inji shi.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa ayyukan ‘yan Boko Haram a garin Geidam ya karu a ‘yan kwanakin nan, musamman ganin cewar sansanonin mayakan ba su da nisa daga garin.

“Suna karbar haraji daga manoma da makiyaya masu tazarar kilomita kadan daga garin kuma babu wanda ya ke iya yin komai akan hakan.”

“Maimakon haka, jami’an tsaro sun sake kafa shingayen binciken ababen hawa 17 cikin garin, inda kuma suke karbar wani abu a hannun ‘yan kasuwar da ke shigo da kayayyaki ta wannan hanya.

“Muna cikin tsaka mai wuya a wannan garin,” inji daya daga cikin ‘yan kasuwar garin da ya nemi a sakaya sunansa.