Labarai

’Yan Bindiga Sun Kashe Dagaci Sun Sace Jama’arsa A Neja

’Yan Bindiga Sun Kashe Dagaci Sun Sace Jama’arsa A Neja

’Yan Bindiga Sun Kashe Dagaci Sun Sace Jama’arsa A Neja

’Yan Bindiga Sun Kashe Dagaci Sun Sace Jama’arsa A Neja » Alfijir

    Daga Abubakar Akote, Minna Da Sagir Kano Saleh

’Yan bindiga sun harbe wani dagaci har lahira sannan suka yi awon gaba da jama’a da dabbobi a yankinsa a Jihar Neja.

A cikin daren Talata ne ’yan bindiga suka kutsa yankin Zazzaga da kewaye da ke Karamar Hukumar Munya, inda suka bindige Dagacin Zazzaga, Malam Usman Sarki, suka sace mutane.

Aminiya ta samu rahoto cewa daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da mata, kuma kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Majiyarmu ta ce “A cikin daren Talata suka kawo harin suka harbe Dagacin Zazzaga, Malam Usman Sarki suka sace shanu suka kuma yi garkuwa da mutane da yawa, wadanda kawo yanzu ba za mu iya cewa ga iya yawansu ba.”

Wata majiyar ta ce, “Ba zan iya cewa ga iya yawan wadanda aka tafi da su ba, saboda da dare abin ya faru kuma mutane sun tsere zuwa cikin jeji, amma dai maharan sun yi awon gaba da mutane da yawa.

“A kauyennmu, Kutara da ke kusa da Zazzaga kadai, na san an sace mutun bakwai ciki har da mata, sannan aka hada da dabbobi.”

Mazauna sun shaida wa wakilinmu cewa a cikin ’yan makonin nan harin ’yan bindiga ya zama ruwan dare a kauyukansu da ke kananan hukumomin Munya da Rafi, inda kusan kullum sai ’yan ta’addan sun kai hari.

Kakakin ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da harin, amma babu cikakken bayani.