Labarai

Yadda za ku gane cewa kuna fama da matsalar kwakwalwa

Yadda za ku gane cewa kuna fama da matsalar kwakwalwa

Kowane dan’adam yana da abin da kan tantance lafiyar kwakwalwarsa. Ya ƙunshi jin daɗin zukatanmu zuciyarmu da tunani, da zamantakewa, kuma yana shafar yadda muke tunani, da ji, da kuma gudanar da ayyukan yau da kullum.

 

Haka nan yana taimakawa wurin sanin yadda za mu magance damuwa, alaƙa da wasu, da kuma yin zaɓi tsakanin abubuwa.

 

Mece ce matsalar ƙwaƙwalwa?

An rarraba matsalar ƙwaƙwalwa zuwa kashi-kashi domin taimaka wa masana wurin sanin irin kulawar da mutane ke bukata.

 

An raba alamun matsalar kwakwalwa zuwa manyan gidaje biyu – wanda ya shafi dabi’a da kuma wanda ya shafi hankali.

 

Alamun da suka shafi dabi’a su ne yanayin da mutum kan kai makura ta dabi’un dan’adam, kamar cutar damuwa da kuma ta zakuwa.

 

Alamun matsalolin ƙwaƙwalwa da suka shafi hankali kuwa suna shafar kusan mutum ɗaya cikin 100 kuma abin da waɗannan ke yi shi ne suna dagula wa mutum hanyoyin tantance ainihin abubuwan da ke faruwa a zahiri, suna kawo cikas ga tunanin mutum da kuma hukunce-hukuncen da yakan zartas.

 

Irin wadannan sun hada da tabuwar hankali da kuma sauyi a yanayin halayya cikin kankanin lokaci.

 

Mene ne ke haifar da matsalolin kwakwalwa?

 

Ba a san ainihin abin da ke haifar da yawancin matsalolin ƙwaƙwalwa ba amma ana tunanin abubuwan da suke faruwa a zahiri da tunani da kuma muhalli suna taka rawa sosai.

 

Yawancin cututtuka na tabin hankali ana alakanta su da gado, wato suna iya bibiyar wadanda suka fito cikin wannan iyalin, wanda ke nuna alaƙar su da kwayoyin halittun gado.

 

Masana sun yi imanin cewa yawancin cututtuka na tabin hankali suna da alaƙa da matsalolin da ke shafar kwayoyin halittar dan’adam, wadanda ke zamowa silar matsaloli tun daga farko, sai dai zai iya yiwuwa ba su ne za su haifar da matsalar ba kai-tsaye.

 

Shi ya sa mutum zai iya gadon abubuwan da kan iya haifar da wata matsala amma wata kila ba zai yi fama da matsalar ba.

 

Sai dai yanayin rayuwa kan iya tsokalo wadancan matsaloli ta yadda za su iya haifar wa mutum tabin hankali.

 

A cewar kungiyar Charity Mind waɗannan abubuwan na iya haifar da matsalar kwakwalwa:

 

Ta yaya ake gano matsalolin ƙwaƙwalwa?

Ba za a iya gani matsalar kwakwalwa ta hanyar gwajin jini ko wani riwa na jikin dan’adam ba.

 

A maimakon haka, kwararrun likitocin masu lalurar kwakwalwa ko kuma masana halayyar dan’adam ne suke iya gano ta.

 

Sukan gano matsalar ce ta hanyar nazartar alamomi da kuma lura da mutane na wani tsawon lokaci.

 

Yawancin matsalolin ƙwaƙwalwa na da alamomi masu kama da juna, shi ya sa ake wahala wajen tantance takamaiman matsalar kwakwalwa da ke addabar mutum.

 

Yaya ake magance matsalar kwakwalwa?

Akwai manyan hanyoyi biyu da ake bi wajen magance matsalar keakwalwa – Ta hanyar tattaunawa da kuma ta hanyar magunguna.

 

Hanyar tattaunawa ta kunshi tattauna matsalolin da mutum ke fusknata tare da wani kwararre. Matsalolin za su ksance wadanda suka shafi lafiya kwakwwar mutum.

 

Sai kuma wata hanyar da ake kira ‘Psychotherapy’ a turance, wadda ita ma wata hanya ce ta tattaunawa. A irin wannan yanayi ana tattaunawa ne kan abubuwan da suka faru tun farkon rayuwar mutum da kuma yadda suke yin tasiri ga rayuwarsa ta yanzu.

 

Dangane da magunguna kuwa, akan yi amfani da magunguna kashi hudu, akwai na rage damuwa, da masu rage zaƙuwa, da masu daidaita tunani da kuma magunguna masu daidaita yanayi.

 

Yawanci akan bai wa masu cutar tsananin damuwa da kuma zukuwa magungunan rage damuwa.