Labarai

Yadda ‘siniya ya yanka makogoron’ wani dalibi a makarantar kwana a Borno

Yadda 'siniya ya yanka makogoron' wani dalibi a makarantar kwana a Borno

Ƴan uwan wani ɗalibi da ke Kwalejin Elkanemi College of Theology A jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ne, suke neman mahukunta su gudanar da bincike a kan wani mummunan raunin da aka yi wa Ɗalibin.

 

Ƴan uwan dai suna zargin wani Ɗalibi da ke ajin gaba da na Jibrin ne ya raunata shi a wuya ta hanyar yankansa da reza har sai dai ya yi illa ga maƙogwaronsa.

 

Ƴan uwan ɗalibin mai suna Jibril Sadi Mato, wanda ake yi wa laƙabi da Ramadan, ɗan shekara 11 da haihuwa, sun yi zargin cewa wani dan ajin gaba da shi ne a makarantarsu ne ya yayyanka shi da reza a wuya, sakamakon fusatar da ya yi saboda Jibril ɗin ya ƙi zuwa wani aiken da ya yi masa.

 

Kuma a halin da ake ciki yana kwance a asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, a sashen da ake samar da kulawa ta musamman ga majinyata.

 

Wata makusanciyar mara lafiyar ta ce: “Ramadan an yanke shi ne a wuya, wanda hakan ya haifar masa da raununka masu tsanani, a halin da ake ciki yana kwance a asibiti rai hannun Allah.

 

Kuma bayanan bincike na nuna ko da ya tashi daga jinyar ba lallai ya sake ci gaba da iya magana ba, idan ma har ya tashin kenan.

 

“Kuma wanda ya aikata masa hakan ma yaro ne ɗan makarantarsu ya yanka shi da wuƙa ya masa wannan illar amma kuma ana so a ɓoye abin, don ita kanta hukumar makaranta ba ta sanar da faruwar hakan ba.

 

“Muna so gwamnati ta yi bincike ta gano ainhin abin da ya faru sannan a gurfanar da mai laifin a kuma yi masa hukunci,” kamar yadda ta faɗa.

 

Binciken da dangin Jibril suka yi, ya nuna cewa ɗan ajin gaba da shi da ya yi masa raunin, wanda aka ce yana aji biyu a sashen manya, wato SS2, wani ɗan gata ne da ya fito daga gidan masu hannu da shuni – kuma wannan ne ya sa, kamar yadda suke zargi, shugabannin makarantar suke ta rufe maganar.

 

Wata ruwayar ma ta ce shugabannin makarantar sun fara sauya maganar, suna cewa wai rauni kawai Ramadan ya ji, ba wani ne ya cutar da shi ba.

 

Kazalika wasu rahotanni, sun yi zargin cewa ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan cin-zali ko fin ƙarfi da manyan ɗalibai suke nuna wa ƙanana a makarantar ba, amma kawo yanzu babu wani mataki da aka ɗauka na ladabtar da irin waɗannan ɗalibai da ake zargi.

 

Mun yi ƙoƙarin tuntuɓar shugabannin kwalejin ta waya, amma hakan bai samu ba. Kazalika mun tura musu sako a rubutacce, amma shiru kake ji.

 

BBC dai a shirye take ta ba su dama don jin nasu bangaren, idan sun shirya.

 

Kazalika mun nemi ɓangaren rundunar ƴan sanda a jihar Borno, wato kakakinta, Sufurtanda Kamilu Sha Tambaya, tare da tura masa saƙo ta waya, shi ma bai samu ba a lokacin haɗa wannan rahoton.

 

Sai dai yayin da ake jira a ga yadda mahukunta za su ɓullo wa wannan lamari, ƴan uwan ɗalibin da aka yi wa raunin, wato Jibrin Sadi Mato, sun buƙaci mahukunta a jihar Bornon da su taimaka wajen jinyar dalibin.

 

“Muna kira da a taimaka mana wajen lafiyar Ramadan, a daauke shi a kai shi wajen da zai samu lafiya da wuri, inda hali ma a kai shi ƙasar waje don yana cikin wani yanayi mai tsanani,” in ji makusanciyar tasa.

 

A Najeriya dai, a ƴan shekarun nan ana samun wannan matsala ta cin zalin ko fin ƙarfi da wasu ɗalibai suke nuna wa na ƙasa da su.

 

Ko a ƴan makwannin da suka wace an ba da labarin wani ɗalibi da aka azabtar da shi a wata makaranta a Legos, har ta kai ga rasuwarsa.

 

A Abuja, babban birnin tarayyar ma, haka ta faru a wata makaranta, inda mahukunta suka ce suna gudanar da bincike.

 

Amma kawo yanzu babu wani hukunci da za a iya nunawa a matsayin abin misali da zai taka birki ko ya zama ishara ga musa irin wannan aika-aikar.