Labarai

Yadda matan da suka haihu ba tare da miji ba ke more rayuwa a China

Yadda matan da suka haihu ba tare da miji ba ke more rayuwa a China

Yadda matan da suka haihu ba tare da miji ba ke more rayuwa a China

china
Bayanan hoto,Zhang Meili ta tsara yadda za ta kula da yaron ta Heng Heng tare da tallafawar mahaifiyarta

  • Marubuci,Stephen McDonell
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari,China correspondent

A shekarun baya, yana da matuƙar wahala mace marar aure ta iya zama uwa a China, amma a yanzu tun daga al’adun mutanen ƙasar har zuwa dokokin ƙasar sun fara sauyawa.

A cikin gidanta da ke Shanghai, Zhang Meili ta saɓa yaronta a kafaɗa tana shafa bayan shi, yanayin sa ya nuna yana cikin farin ciki, ta ci gaba da shafa bayan shi tana masa bayanin cewa ta kusa fara fita domin nemo nemo masa kuɗi.

Bayan Mahaifiyar yaron ɗan wata biyu, Heng Heng, yana samun kulawar kakarsa, wadda ta dawo gidan domin taimaka wa ɗiyarta wajen kula da jikanta.

Rayuwar Heng Heng na tafiya ne ba tare da mahaifi ba, lamarin da ya shafi yara da dama a China, musamman yankin karkara.

Yaƙinin da ake da shi cewa, bai kamata yara suna girma ba tsakanin mahaifansu biyu ba ya fara zama tarihi a nan.

Zhang Meili at ce ta yi farin ciki sosai da ta samu damar dawowa cikin birnin Shanghai domin yin kasuwanci, saboda haihuwa batare da aure ba a wannan birni an yarda da hakan.

“Naji daɗi sosai na kuma gode da damar da ake ba irin mu a Shanghai, saboda na fito daga ƙauyen Henan, kuma a can ana nuna ƙyama da wariya ga ire-iren mu.”

Jariri Heng Heng zai girma a birnin shanghai da ba a cika tsangwamar yara marasa uba ba.
Bayanan hoto,Jariri Heng Heng zai girma a birnin shanghai da ba a cika tsangwamar yara marasa uba ba.

Zhang Meili ta zama uwa wadda za ta kula da jaririnta ba tare da taimakon mahaifin yaron ba, bayan da iyalan saurayin ta suka ƙi amincewa da ita a matsayin wadda zai aura, saboda suna ganin wayewar iyalan ta ta yi yawa.

Wannan dalilin ne ya sanya saurayinta ya rabu da ita , duk da yasan tana ɗauke da cikinsa.

Wakilin BBC ya tambayi mahaifiyar ta ko ya ta ji da ta samu labarin cikin da ɗiyarta yar shekaru 25 ke ɗauke da shi, sai ta ce “ya na ji? na shiga tashin hankali, saboda akwai wahala sosai kula da yaro ba tare da taimakon mahaifinsa ba, ga kuma cin fuska da ake fuskanta daga makwabta.”

Amma da aka haife shi yanzu kike ganinsa ya kike ji?

Cikin fara’a da annashuwa ta ce ” A yanzu da nake ganinsa inajin dadi matuƙa”.

Zhang Meili ta na da mafitar da bakowace uwa da ke cikin halin irin na ta ke da ita ba, saboda tana da sana’a.

Wannan shine abin da ya bata ƙwarin guiwar samun kula da rayuwar ta.

Tana da shagon tausa koda yake kasuwancin yanzu yake farfaɗowa daga illar da kullen korona taya kuma neman a karɓeta a matsayin wadda ke da yaro ba tare da aure ba.

Ba a abi mai sauƙi ba ne Zhang Meili ta iya cimma burin ta na bunƙasa sana’arta, saboda irin ƙalubalen da za ta iya cin karo da su a matsayinta na wadda ke ɗaukar ɗawainiyar jaririnta.

Ta ce abokananta duk basu goyi bayan matakin da ta ɗauka na haihuwar cikin da ta ɗauka ba. Sun bata dalilin cewa hakan zai sanya ta gamu da cikas wajen samun mijin aure nan gaba, kuma bai dace yaro ya rayu ba tare da mahaifinsa ba.

Sana'ar da Zhang Meili ita ce ta bata Kwarin guiwar samun ƴancin kanta.
Bayanan hoto,Sana’ar da Zhang Meili ita ce ta bata Kwarin guiwar samun ƴancin kanta.

“Lokacin da nake da ciki, ni kaɗai nake zuwa asibiti, a duk lokacin da naga wata taje tare da mijinta inajin kishi da haushi,”inji ta.

“Amma na zaɓi na zama uwa mai zaman kanta. na kuma zaɓe shi, saboda haka ina buƙatar na kauda duk irin waɗanan damuwar.”

Sai dai ba kallon da mutane ke yiwa wadda ta haihu batare da miji kaɗai ne matsalar da ta sanya hakan ke da wahala ba.

Ko a 2016, gwamnatin China ta bada umarnin hana hukumomi bayar da takardar haihuwa ga yaran da aka haifa batare da aure ba.

Kuma duk lokacin da ake neman takardar haihuwa sai an gabatar da takardar shaidar aure da kuma takardar shaidar zama ɗan ƙasa na mahaifan jaririn biyu.

Takardar shaidar haihuwa ita ce takardar da ake saka yaro makaranta da ita.

Wakilin BBC ya ce “A lokacin da nazo China shekaru ashirin da suka gabata zani iya tuna yadda matan da sukayi ciki suka riƙa cewa basu da wani zaɓi wanda ya wuce su zubar da cikin, saboda a ƙasar duk yaron da bashi da takardun da ake buƙata, yana shan wahalar rayuwa.”

Ko bayan da gwamnati ta canza wannan doka, da wuya matan da basu da aure suyi ciki saboda tsoron yadda zasu samu kuɗin kula dalafiyar yaron nasu da kuma samun hutun haihuwa a wajen aikin su ba tare da an tsaida masu albashi ba.

Yanzu haka dai an canza dukkan waɗannan dokoki koda yake dai akwai buƙatar kamfanin da suke ma aikin ya aika a rubuce domin neman izini daga gwamnati, kuma wasu kamfanoni basu cika amincewa da irin wannan buƙata ba.

Wani lauya da ke aiki kan irin wannan matsalar, ya shaidawa BBC cewa yana da wata da yake karewa kan hanasamun hutun haihuwa ba tare da tsaida mata albashi ba, wanda bata samu damar hakan ba sai bayan da ta yi ƙarar kamfanin sannan suka amince.

“Hakan ya danganta da kamfanin da kuma wayewar kan kamfanin a ɓangaren kare haƙƙin ma’aikatansu, wasu shugabannin kamfanonin basu fahimci dokar yadda ya kamata ba.”

Wasu basu bincike kan dokokin da ake sabuntawa shiyasa suke ɗaukar hakan a matsayin wani babban laifi.

fg
Bayanan hoto,Akwai yiwuwar China za ta ƙara yawan haihuwa a ƙasar, sai dai duk da hakan matan dake haihuwa ba tare da aure ba ka iya ci gaba da fuskantar wariya.

Farfesa Yang Juhua dake jami’ar Minzu a Beijing ya ce “A ƙarƙashin dokar China, dukkan wata uwa da yaranta ɗaya ne babu ruwan doka da hanyar da ta haihu.”

“Sai dai wajen zartar da dokar ana cin karo da cikas, saboda da yawan mutane basu amanna da haihuwa ba tare da mijin ba.”

Ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya hukumomi sauya ra’ayi kan hakan shine, ƙarancin haihuwa da ƙasar ke fuskanta tun bayan dokar haihuwar yaro guda da ƙasar ta sanya shekaru masu yawa.

Hukumomi sun dawo suna kira da mata su riƙa haihuwa sai dai da yawan basu ansa kiran ba saboda yanayin tatalin arziƙi.

Peng Qingqing na ɗauke da tsohon ciki kuma bata da aure amman tana kasuwanci kamar Zhang Meili, ta kuma ce hakan ne ya taimaka mata wajne kula da kan ta.

Peng Qingqing  yar kasuwa ce kuma zata zama uwa nan ba da jimawa ba.
Bayanan hoto,Peng Qingqing yar kasuwa ce kuma zata zama uwa nan ba da jimawa ba.

“Mahaifiya ta kullum tana faɗi mani cewa ya kamata kowace mace ta kasance tana da ƙwarin gwiwa, ta zama ta tsayu da ƙafafun ta, saboda haka banison nayi aure kawai saboda na haihu.

Yar shekaru 30 ɗin ta ce a lokcin da ta samu ciki ba ta shirya yin aure ba, wani saurayin ta ne ƙaramin yaro yayi mata cikin sai kawai ta ji nason haife cikin.

Peng Qingqing ta ce lokacin da ta samu ciki bata shirya yin aure ba.
Bayanan hoto,Peng Qingqing ta ce lokacin da ta samu ciki bata shirya yin aure ba.

Zhang Meili ta ce haihuwa ba tare da miji ba wanan zaɓi ne na mata da kansu, su za su ga minene suke ra’ayi ba gwamnati ko wasu mutane ba.

BBC ta tambaye ta daga ƙarshe wace shawara zata ba sauran matan da suka tsinci kansu cikin irin wannan halin, sai tace, ” Ya danganta da halin da take ciki, amman indai tana son yara to ta haife cikin kada ta zubar.”

“Kada ki bari ki rasa ɗan ki saboda maganganun mutane ko tunanin kallon da za a maki a cikin al’umma.”