Labarai

Yadda jarabar shan ƙwaya ta jefa Shi wannan yanayin

Yadda jarabar shan ƙwaya ta jefa Shi wannan yanayin

Miliyoyin mutane ne suka jarabtu da shan miyagun ƙwayoyi a yankin Kashmir da ke Indiya.

 

An yi ƙiyasin cewa ana kwantar da mutum guda a asibiti cikin kowane mintuna 12 sakamakon dalilin shan miyagun ƙwayoyi a wannan shekara a yankin.

 

Ayesha(ba sunanta ne na gaskiya ba) matashiya ce mai shekara 18, ta kuma jarabtu da shan ƙwayar heroin da tabar wiwi cikin shekara uku da suka gabata.

 

Ta ce “da farko wasu ƙawaye na ne a makaranta suka riƙa ba ni ƙwayar a kyauta, amma da na saba da ita har roƙonsu ƙwayar na riƙa yi”.

 

Ayesha da ƙawayenta kan ɓuya a maƙabartu domin yin shaye-shayensu.

 

Ta yi bayani kan yadda ta jarabtu da shan ƙwaya, “Idan muka nemi kudi a wajen iyayenmu, ba mu samu ba, mukan shiga damuwa”.

 

“Na yi tunanin na fara sata, amma ina tsoron abin da zai iya faruwa, ina da wayar iPhone amma na sayar da ita, nakan ranci kuɗi daga wajen ƙawayena.”

 

Cibiyar lura da lafiyar ƙwaƙwalwar da Kashmir da aka fi sani da Imhanz t gudanar da wani bincike a gundumomin yankin 10 cikin watan Maris da ya gabata.

 

Daga cikin binciken da cibiyar ta yi ta gano cewa matasan da ke buguwa da hodar heroin da ƙwayar ganja na da yawan gaske.

 

Ma’aikatar kula da walwalar jama’a, hadi da gwamnatin Indiya, sun gudanar da wani bincike cikin watan Maris na wanna shekara, wanda sakamakonsa ya nuna cewa yankunan Jammu da Kashmir na da fiye da mutum miliyan guda da suka jarabtu da shan miyagun ƙwayoyi, ciki har da mata fiye da 100,000.

 

Muzmal (Ba sunanta na gaskiya ba) ƙawa ce ga Ayesha, ta ce ta jarabtu da shan ƙwaya ne a lokacin kullen korona. “Wasu daga cikin ƙawaye na kan sha miyagun ƙwayoyi a gaba, a lokacin ban san daɗinta ba”, in ji Muzamil.

 

Wani matashin mai suna Muzamil ya ce “a lokacin kullen korona, lokacin da komai ke rufe, nakan ji na gundura da komai, sai na fara shan wiwi kaɗan-kaɗan, daga nan na fara yin allurar ƙwayar heroin, sai na riƙa jin nishaɗi da annashuwa”.

 

Muzamil ya ce iyayensa sun ba shi kyautar mota a bikin zagayowar ranar haihuwarsa, “to amma da kuɗi suka yi min ƙaranci, basuka suka yi min yawa, na sayar da wayata, sai ya yanke shawar sayar da motar.”

 

Daga ƙarshe ‘yan sanda sun kama Muzamil, mai shekara 23 da ƙwaya, sannan aka yanke masa hukunci daurin shekara guda a gidan kaso.

 

Fiye da mata 100,000 ne suka jarabtu da ƙwaya a Kashmir

‘A lokacin da na fito daga gidan yari na shiga damuwa, daga baya iyayena sun kai ni cibiyar sauya tunani, bayan shafe wasu watanni ina karɓar horo a cibiyar, na samu sauƙi, amma duk da haka nakan tuna irin bakin duhun da na gani a gidan yarin.

 

“Ko yanzu nakan ji tsoro”. Gwamnatin ƙasar ta samar da cibiyoyin sauya tunani ga mutanen da suka arabtu da shan miyagun ƙwayoyi a gundumomi takwas daga cikin gundumomin Kahmir 10 inda dubban matasa ke samun horo a kowace rana.

 

A daya daga cikin cibiyoyin da ke gundumar Srinagar, likitoci sun ce tsakanin watan Maris na shekarar 2022 zuwa watan Maris na 2023 matasa 41,110 ne suka samu horo a cibiyar.

 

Hakan na nufin cikin kowanne minti 12 ana kai matashi guda cibiyar a tsakanin wannan lokaci.

 

”A yanzu jarabtuwa da shan miyagun ƙwayoyi na neman zama wata annoba”, kamar yadda Zoya Mir, wata likitar ƙwaƙwalwa ya shaida wa BBC.

 

Zoya Mir ta ce ta horas da matasa masu yawa a cibiyar.

 

Ta ce ”nakan yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi tun daga ƙarfe 10 na safe zuwa 7 na maraice, masata ne ke zuwa cibiyar da ke bukatar kulawa.”

 

“Da yawa sun warke, da yawa daga cikin wadanda suka jarabtu da ƙwayar maza ne, amma akwai mata masu yawa a ciki waɗanda shekarunsu suka kama daga 13 zuwa 40”, in ji shi.

 

Ta ce binciken da suka gabatar ya gano cewa a yanzu yankunan Jammu da Kashmir sun zarta yankin Punjab a yawan masu shan ƙwaya.

 

“Kuma abin da zai baka mamaki shi ne kashi takwas ne kawai masu shaye-shayen marasa ilimi, sauran duka masu ilimi ne, abin da nuna cewa dole mu fara gangamin wayar da kai tun daga makarantu”.

 

Jami’an taro da dama ciki har da ‘yan anda ne ke aiki domin yaƙi da yaɗuwar miyagun ƙwayoyi a yankin Kashmir.

 

Wani jami’i ya ce shekara 100 da suka gabata, yankin Kashmir ya kasance matattarar cinikayyar ƙwaya a duniya.

 

Shi ma wani jami’ai da bai amince a ambaci sunansa ba ya ce abin da ke faruwa a yanki a yanzu ba a taɓa ganin irinsa ba.

 

Ya ce daga shekarar 1990 zuwa 2000 matasa kan sha ƙwayoyin barci ko na kashe zafin ciwo.

 

Cinikin hodar heroin na ci gaba da ƙaruwa a yankin sakamkon yawan buƙatarsa.

 

Shugaban rundunar ‘yan sandan yankin Dilbagh Singh ya bayyana matsalar ƙwaya da cewa ta zarta ayyukan ‘yan bindiga.

 

Ya yi zargin cewa Pakistan ce ke ƙara rura wutar cinikayyar ƙwaya a yankin Kashmir.

 

To amma hukumomin Pakistan sun sha musanta wanna zargi a baya.