Labarai

WATA SABUWA: Hukumar Hisbah Ta Dakatar Da Auren Wata Budurwa Da Saurayinta.

Hukumar Hisba ta dakatar da auren wata Budurwa Daga Cikin Waɗanda Za’a Daurawa Sure A yau Juma’a.

 

Wata Budurwa a unguwar Kawo Dake karamar Hukumar Nasawara kenan da Hukumar Hisba ta Dakatar da aurensu da angonta da aka shiryabyi a gobe Juma’a sakamakon yadda angon na ta Abubakar Abdullahi ya chanja ta da wata Budurwar ba tare da sanin Hukumar Hisba ba.

 

babban abinda yaja hankalin Kwamandan Hisba Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shine, yadda aka zargi wannan ango da karbar Katin shaidar bada kayan Daki daga wajen Budurwar da aka tantancesu tare.

 

Tunnda farko dai Abubakar ya mika Katin karbar kayan dakin ne ga budurwar ta sa ta farko Wacce yake so ya aura a Auren Gata da Hukumar Hisba zatayi a yau juma’a idan Allah ya kaimu, Saidai a yanzu haka hukumar ta Hisba ta dakatar da auren Abubakar nan take bayan da budurwar tayi korafi a Rahma Radio zuwa Hukumar Hisba.

 

“Shekararmu 3 Muna soyayya dashi” Cewar Amarya da ake Neman yaudara a zantawarta da Rahama Radio.