Labarai

Wani Ba’amurke ya kashe yaro ɗan shekara 6 saboda ƙin jinin Musulunci

Wani Ba'amurke ya kashe yaro ɗan shekara 6 saboda ƙin jinin Musulunci

A kasar Amurka. ana tuhumar wani mutum da laifin kisan kai da kuma nuna ƙiyayya bayan da aka zarge shi da caka wa wasu mutane biyu wuƙa saboda su musulmai ne.

 

Ana zargin Joseph Czuba mai shekaru 71 da kashe wani yaro dan shekara shida da raunata wata mata mai shekaru 32 a Plainfield, Illinois da ke Amurka.

 

Ofishin babban jami’in ƴan sanda na yankin Will County ya ce an kai musu hari ne saboda rikicin da ake yi a yanzu tsakanin Hamas da Isra’ila.

 

Shugaba Biden ya ce ya ji “bacin rai” kan harin da aka kai wa mahaifiyar da danta, waɗanda Falasdinawa ne mazauna ƙasar Amurka.

 

“Wannan mummunan aiki na ƙiyayya ba shi da gurbi a Amurka, kuma ya ci karo da aƙidunmu,” in ji Biden a cikin wata sanarwa.

 

“A matsayinmu na Amurkawa, dole ne mu hadu wuri guda, mu yi watsi da kyamar Musulunci da duk wani nau’i na son zuciya da kiyayya.”

 

A cikin sanarwar ta ranar Lahadi, ofishin ƴan sandan na Will County ya ce a safiyar Asabar sun samu kiran gaggawa daga matar wadda ta ce wanda ya ba su hayar gida ne ya kai mata hari a yankin Plainfield, kusa da Chicago.