Labarai

Wajabcin Biyan Mai wankin Takalmi a Bakin Masallaci bada Izinin Mai Takalmi ba

IDAN SHUSHAINA YA WANKE TAKALMANA A KOFAR MASALLACI, BADA IZNI NA BA, YA WAJABA NA BIYA SHI

Wajabcin Biyan Mai wankin Takalmi a Bakin Masallaci bada Izinin Mai Takalmi ba kamar yadda wasu Masu wankin takalma kanyi a Masallatan Cikin gari da Tasha.

Tambaya

Àllah Ya taimaki malam, na ajjiye takalmi na shiga sallah, kafin na fito sai na samu SHUSHAINA ya wanke shi, ya yi musu foolish, shin dole na biya shi ?

Wajabcin Biyan Mai Wankin Takalmi bayan bakuyi Magana ba

Amsa

Wa alaikumus salam, To Dan’uwa mutukar ba da izninka ya yi ba, ba sai ka biya shi ba, Annabi (SAW) yana cewa “Ana gina ciniki ne akan yarjejeniya”, Kai Kuma ga shi ba ku daddale ba kafin ya yi, Aya ta (29) a cikin suratun Nisa’i ta kunshi ma’anar wannan hadisin.

Sai dai biyan kudin saboda kyautatawa, yana iya zama mustahabbi, saboda yawancinsu talakawa ne, Allah Yana cikin taimakon bawa mutukar bawan yana cikin taimakon da’nuwansa.

Sai dai biyan kudin saboda kyautatawa, yana iya zama mustahabbi, saboda yawancinsu talakawa ne, Allah Yana cikin taimakon bawa mutukar bawan yana cikin taimakon da’nuwansa.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

17/05/2023