Labarai

Waiwaye: Ranar yanke hukunci kan ƙarar Atiku, ƙungiyar ƙwadago ta bai wa gwamnoni wa'adi kan albashi

Waiwaye: Ranar yanke hukunci kan ƙarar Atiku, ƙungiyar ƙwadago ta bai wa gwamnoni wa'adi kan albashi

Waiwaye: Ranar yanke hukunci kan ƙarar Atiku, ƙungiyar ƙwadago ta bai wa gwamnoni wa’adi kan albashi

Kamar kowane mako, mun duba wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata.

Kotun Kolin Najeriya ta sa ranar fara shari’ar zabe tsakanin Atiku da Tinubu

Atiku Abubakar

ASALIN HOTON,TWITTER/ATIKU ABUBAKAR

Kotun Kolin Najeriya ta sanya ranar Litinin, 23 ga watan Oktoba, don fara sauraron ƙarar da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya daukaka a kan zaben 2023.

Wata sanarwa da magatakardar kotun, Zainab M. Garba, ta sanya wa hannu ta zayyana hukumar zabe ta INEC da wasu a matsayin wadanda ake kara.

Atiku Abubakar dai ya yi alkawarin daukaka kara ne a kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe na ranar 6 ga watan Satumba da ya tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu.

Jagoran adawar na Najeriya ya samo ƙarin shaida a kan karar da ya shiga yana kalubalantar cancantar Tinubu, inda yake fatan Kotun Kolin za ta ba shi damar gabatar da ita, yayin da take sauraron shari’arsa.

Hukumar zabe ta INEC ta ayyana cewa Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya samu kuri’a 8,794,726, yayin da ta ce Atiku Abubakar ya samu kuri’a 6,984,520.

Sai dai a karar da ya daukaka gaban Kotun Kolin, Atiku ya shigar da hujjoji guda 35, wadanda yake cewa bisa la’akari da su, kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a karkashin Mai shari’a Haruna Tsammani ta “tafka babban kuskure”.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a takardar daukakar da babban lauyan dan takarar na PDP, Chris Uche ya shigar, Atiku Abubakar ya roki kotun ta jingine duk abubuwan da kotun zaben shugaban kasa ta gano da kuma matsayar da ta cimma.

Tinubu ya ba da umarni a biya malaman jami’a albashi na watannin yajin aiki

Bola Tinubu

ASALIN HOTON,STATE HOUSE

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin biyan malaman Jami’a ta ASUU albashinsu da aka riƙe lokacin da suke yajin aiki.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a, ta ce Tinubu ya kuma jingine batun manufar gwamnati ta ba aiki ba biya da gwamnati tayi kan malaman bayan tsunduma yajin aiki da suka yi na tsawon wata takwas daga 14 ga watan Febrairun 2022 zuwa 17 ga Oktoban 2022.

Sanarwar ta ce shugaban ya yi haka ne domin nuna jin-kai ga malaman.

“A yunƙurinsa na rage matsalolin da ake fuskanta a lokacin aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki a ƙasar nan, tare da amincewa da aiwatar da tsare-tsaren da aka cimma a tattaunawar da aka yi tsakanin ASUU da gwamnatin tarayyar Najeriya, Tinubu ya bayar da umarnin jingine batun ba aiki ba biya, wanda zai bai wa ‘yan ƙungiyar ASUU damar karɓar albashin watanni huɗu daga cikin takwas,” in ji sanarwar.

‘Badaƙalar kwangila ta janyo wa Najeriya asarar tiriliyan 2.9 cikin shekara uku’

EFCC

ASALIN HOTON,STATE HOUSE

Sabon shugaban Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa a Najeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce ƙasar ta yi asarar naira tiriliyan 2.9 ta hanyar rashin gaskiya a harkar kwangiloli da zamba wajen sayan kayayyakin gwamnati a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Olukoyede ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga Sanatoci a yayin tantance shi domin tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC ranar Laraba.

Ya ce adadin kuɗin ya isa a biya kuɗin gina tituna na aƙalla kilomita 1,000, da gina manyan makarantu kusan 200, da kuma ilimantar da yara kusan 6,000 daga matakin firamare har zuwa jami’a a kan Naira miliyan 16 ga kowane yaro.

Da yake ƙarin haske game da hurumin binciken hukumar, Olukoyede – da Majalisar Dattawan ta tabbatar bayan tantancewar – ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban EFCC yana da ‘yancin gudanar da bincike ga kowa a ƙasar.

Ya kuma yi alƙawarin rashin saɓa ƙa’ida a gudanar da aikinsa, yayin da ya sha alwashin yin aiki da al’ummar Najeriya tare da tabbatar da gaskiya da kuma ɗaukar matakan kariya don rage ƙararrakin da aka daɗe ana yi.

Tinubu ya soke naɗin matashi Imam shugaban FERMA

Imam Kashim Imam

ASALIN HOTON,NTA

Shugaba Bola Tinubu ya soke naɗin Injiniya Imam Kashim Imam a matsayin shugaban hukumar kula da manyan tituna ta Najeriya (FERMA).

Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Alhamis, ba ta faɗi dalilin da ya sa aka soke naɗin nasa ba.

Naɗin Imam ya jawo ce-ce-ku-ce musamman ma a shafukan sada zumunta ganin ba a taɓa naɗa matashi mai ƙarancin shekaru kamarsa a hukumar ta Ferma ba.

Masu sukar naɗin nasa na cewa hukumar tana buƙatar shugabanci na mutum mai ɗimbin ƙwarewa da gogewa saboda muhimmancin aikinta.

Zuwa lokacin hada wanann rahoton, matashin bai ce komai ba.

Ƙungiyar ƙwadago ta ba gwamnoni wa’adin mako biyu kan mafi ƙarancin albashi

'Yan kwadago a Najeriya

ASALIN HOTON,NLC

Ƙungiyar kwadago ta bai wa gwamnonin jihohi wa’adin mako biyu su fara tattaunawa kan batun biyan ƙarancin albashin N35,000 ga ma’aikata a jihohinsu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan wa’adin ya yi daidai da sharuddan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin kwadago suka sanya wa hannu.

Sassan Jihohin ƙungiyoyin ƙwadagon sun ba da wa’adin makonni biyu inda suka tuntubi gwamnonin da su hanzarta aiwatar da shirin biyan ƙarancin albashin.

A wani labarin kuma, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin bada tallafin kudi naira tiriliyan 1 da nufin taimakawa gidaje miliyan 15 domin rage raɗaɗin tattalin arzikin da ake samu na cire tallafin man fetur.

A ƙarkashin wannan shirin, kowane magidanci zai karbi Naira 25,000 na tsawon watanni uku, wanda ya kai kusan naira tiriliyan 1.13.

Ministar ma’aikatar jin ƙai, Dr. Betta Edu, ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 61 ne za su ci gajiyar wannan tallafin kudi.

A baya dai shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun cimma matsaya da gwamnatin tarayya a ranar 1 ga watan Oktoba, inda ta tanadi cewa duk ma’aikatan tarayya za su karbi ƙarancin albashin naira 35,000 daga watan Satumba, har sai an kammala sabon mafi karancin albashi na kasa.

Za a rufe tasoshin motar da ba sa kan ƙa’ida a Abuja saboda ƙaruwar fashi

Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce za ta rufe duka tasoshin motar da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba, a wani mataki na yaƙi da masu fakewa a matsayin direbobi domin yi wa fasinjoji fashi a mota da aka fi sani da ‘One -Chance’.

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da manema labarai.

An samu rahotannin yin fashi da garkuwa da mutane a Abuja tsawon makonni, inda mazauna birnin ke cikin fargaba kan ayyukan ’yan ta’addan da ke fakewa da sana’ar haya don kai hari da kuma yi wa mutane fashi.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa Wike ya ce hukumar FCTA ta kafa rundunar hadin gwiwa kan laifukan da suka shafi kan iyakoki, tare da mai da hankali kan magance ‘yan fashi da makami.

Ministan ya danganta ƙaruwar aikata laifukan da tasoshin motan da ke aiki ba bisa ka’ida ba da kuma gine-ginen da ba a kammala ba waɗanda ke zama mafakar ɓata-garin.

Ya ƙara da cewa, babban birnin tarayya Abuja a tsakiyar jahohin Neja da Kogi da Nasarawa da kuma Kaduna, inda ake fama da matsalar ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Mista Wike ya ce, akwai buƙatar rushe gine-ginen da ba a kammala ba da masu laifi ke amfani da su, domin fatattakar ɓata-garin.

Ministan ya jaddada muhimmancin yin la’akari da illolin tsaro a yayin da ake magance matsalolin da suka shafi tasoshin mota ba bisa ka’ida ba.

Abin da ya sa za mu raba wa kanmu motoci – Majalisar wakilai

Majalisar Dokokin Najeriya

ASALIN HOTON,NATIONAL ASSEMBLY

Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da rahotanni da ke cewa tana shirin sayan motoci domin raba wa mambobinta.

Sai dai ta musanta cewa kuɗin kowane mota zai kai naira miliyan 200.

Mai magana da yawun majalisar Akin Rotimi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce mutane na ta kambama batun sayo motocin wanda kuma ba sabon abu ba ne, a cewarsa.

Tun farko dai a cikin kwanaki da suka gabata an yi ta tafka muhawara kan cewa majalisar wakilan za ta sayo motoci, waɗanda kowace ɗaya kuɗinta ya kai kimanin naira miliyan 200 domin raba wa mambobin.

Duk da cewa mai magana da yawun majalisar bai faɗi kuɗi da kuma irin motoci da za a sayo ba, ya ce abin da take niyyar yi yana bisa tsarin doka, kuma majalisun da suka gabata ma sun yi haka.

Ya ce ko a mafi yawan lokuta “ana saya wa jami’an gwamnati a ɓangaren zartaswa daga matakin darekta zuwa sama, motoci na aiki a ofisoshinsu.”

Karanta cikakken labarin a nan:

Majalisar dattawa ta tabbatar da Olukoyede a matsayin shugaban EFCC

Olukoyede

ASALIN HOTON,FACEBOOK/AJURI NGLALE

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Ola Olukoyede a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Hakazalika majalisar ta tabbatar da nadin Muhammad Hammajoda a matsayin sakataren hukumar.

Tabbatar da mutanen biyu ya biyo bayan tantance su ne da babban zauren majalisar ya yi ranar Laraba kimanin mako guda bayan da shugaba Bola Tinubu ya nada su.

Hakan na nufin an kawo ƙarshen mulkin Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar, wanda har yanzu yake tsare bayan Shugaba Tinubu ya dakatar da shi a watan Yuni.