Labarai

Wadanda Suka Tsira Daga Kwale-Kwalen Da Ya Nutse Da Bakin Haure

Wasu mutane goma sha biyu da suka tsallake rijiya da baya a yunkurin yin kaura ta hanyar teku zuwa Turai sun samu saduwa da iyalansu a Senegal, mako guda bayan an gano su a tekun Atlantika na kasar Cape Verde.

Ana ganin cewa wani jirgin ruwa ne dauke da mutane sama da 100 ya taso daga kasar Senegal zuwa tsibirin Canary na Spain a ranar 10 ga watan Yuli amma bai kai inda ya ke niyya ba. Fiye da bakin haure 60 ne ake fargabar sun mutu sakamakon hantsarin da suka gamu da shi a balaguron.

A makon da ya gabata ne wani jirgin kamun kifi na kasar Spain ya ceto mutane 38 da aka kawo Cape Verde kafin a mayar da su Senegal.

Jami’an Senegal sun ce wani jirgin soji ya maido da maza 37 da suka hada da kananan yara biyar da wani dan kasar Guinea-Bissau, daga tsibirin Sal Island na Cape Verde a ranar Litinin. ‘Yan jaridar Associated Press sun ga wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu an dauke su cikin motocin daukar marasa lafiya a filin jirgin saman Dakar babban birnin Senegal. Mutum daya da ya tsira ya cigaba da kasancewa a asibiti a babban birnin Cape Verde na Praia, a cewar kungiyar agaji ta Red Cross.

Hanyar kaura daga yammacin Afirka zuwa Spain na daya daga cikin hanyoyi mafiya haɗari a duniya, amma duk da haka adadin bakin hauren da ke fitowa daga Senegal a cikin kwale-kwalen katako mara karfi ya karu a cikin shekarar da ta gabata.

KAI-TSAYE
Search
AFIRKA
Senegal Ta Dawo Da Wadanda Suka Tsira Daga Kwale-Kwalen Da Ya Nutse Da Bakin Haure
06:09 Agusta 23, 2023
Hadiza Kyari

Wasu bakin haure da aka ceto

Dubi ra’ayoyi

Wasu mutane goma sha biyu da suka tsallake rijiya da baya a yunkurin yin kaura ta hanyar teku zuwa Turai sun samu saduwa da iyalansu a Senegal, mako guda bayan an gano su a tekun Atlantika na kasar Cape Verde.

WASHINGTON DC —
Ana ganin cewa wani jirgin ruwa ne dauke da mutane sama da 100 ya taso daga kasar Senegal zuwa tsibirin Canary na Spain a ranar 10 ga watan Yuli amma bai kai inda ya ke niyya ba. Fiye da bakin haure 60 ne ake fargabar sun mutu sakamakon hantsarin da suka gamu da shi a balaguron.

A makon da ya gabata ne wani jirgin kamun kifi na kasar Spain ya ceto mutane 38 da aka kawo Cape Verde kafin a mayar da su Senegal.

jirgi cike da bakin haure
Jami’an Senegal sun ce wani jirgin soji ya maido da maza 37 da suka hada da kananan yara biyar da wani dan kasar Guinea-Bissau, daga tsibirin Sal Island na Cape Verde a ranar Litinin. ‘Yan jaridar Associated Press sun ga wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu an dauke su cikin motocin daukar marasa lafiya a filin jirgin saman Dakar babban birnin Senegal. Mutum daya da ya tsira ya cigaba da kasancewa a asibiti a babban birnin Cape Verde na Praia, a cewar kungiyar agaji ta Red Cross.

Hanyar kaura daga yammacin Afirka zuwa Spain na daya daga cikin hanyoyi mafiya haɗari a duniya, amma duk da haka adadin bakin hauren da ke fitowa daga Senegal a cikin kwale-kwalen katako mara karfi ya karu a cikin shekarar da ta gabata.

Kwale-kwale
A cikin watanni shida na farkon shekarar 2023, kusan mutane 800 ne suka mutu ko kuma su ka bace a tekun Atlantika a kokarinsu na isa tsibirin Canary, a cewar kungiyar kare hakkin Spain ta Walking Borders

Annette Seck, Ministar ‘yan kasar Senegal dake zaune a kasashen waje, ta fada a wani taron manema labarai cewa, an binne gawarwakin mutane bakwai da aka gano a cikin kwale-kwalen a wurin a Cape Verde. Ta godewa mahukuntan Cape Verde domin agazawa bakin hauren tare da mika ta’aziyyarta ga iyalan mutanen Senegal din da suka rasa rayukansu.

Masunta da manoma a Fass Boye sun dora alhakin kasadar da matasa su ke yi su sadaukar da rayukansu ta wajen tfiya cikin kwale-kwale da ya yi mummunan cunkoso kan rashin aikin yi.

A cewar Seck, akalla manyan kwale-kwalen kamun kifi guda 20 da ake kira pirogues cike da bakin haure sun bar garin cikin shekaru ashirin da suka gabata.