Labarai

Tasiri biyar na zanga-zangar ‘A Bar Talaka Ya Numfasa a Najeriya

Tasiri biyar na zanga-zangar 'A Bar Talaka Ya Numfasa a Najeriya

Duk da raɗe-raɗin janyewa ko kuma fuskantar cikas kafin wayewar gari, ‘yan ƙwadago a Najeriya sun yi nasarar gudanar da zanga-zangar da ta karaɗe faɗin ƙasar a ranar Laraba.

Babbar manufarsu ita ce nuna adawa da cire tallafin man fetur wanda suka ce shi ne ummul-aba’isin tsadar rayuwa da hauhawar farashin da ba a taɓa ganin irinsa ba cikin ‘yan shekarun nan a Najeriya.

Ba a dai ga wani yunƙuri daga masu zanga-zangar na tunkarar fadar shugaban ƙasa da buƙatun da suka ce, su ne ke ci musu tuwo a ƙwarya ba, duk da yake a wasu jihohi, sun kai ƙorafi ga gwamnoni.

Ƙololuwar zanga-zangar shi ne lokacin da shugabannin ƙwadago suka jagoranci mambobinsu zuwa harabar Majalisar Dokoki ta Tarayya, lamarin da ya kai ga ja-in-jar da ta karya ƙofar shiga majalisa.

Tun a jajiberen wannan zanga-zanga, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargaɗi ƙungiyoyin ƙwadagon da cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kai ga tashin hankali ba.

Wata sanarwar da shugabannin ƙwadagon suka fitar bayan kammala zanga-zangar ta jinjina wa al’ummar Najeriya a kan goyon bayan da suka nuna.

Ta ce: “Saƙon da kuka aika yau, manuniya ce mai ƙarfi ta ƙudurinmu duka a matsayin ‘yan kishin ƙasa kuma waɗanda suka mallaki babbar niyyar da za su nemi sai lallai masu mulki sun saurare mu”.

Zuwa yanzu dai, babu ko ɗaya a cikin manyan buƙatun ‘yan ƙwadagon suka gabatar, da za a bugi ƙirji a ce an biya musu, amma duk da haka ana iya cewa zanga-zangar ta cimma nasarori.

Ga biyar daga cikin tasirin da muka lura da su na zanga-zangar da ‘yan ƙwadagon suka yi wa taken ‘A Bar Talaka Ya Numfasa’;

Ganawa da Tinubu

Wata nasara da za a iya cewa zanga-zangar ‘yan ƙwadago ta cimma, ita ce samun damar ganawar ƙeƙe-da-ƙeƙe da jagororin ƙwadagon, Kwamared Joe Ajero na NLC da takwaransa Festus Osifo na TUC suka yi da Shugaba Bola Tinubu.

Shugaban na Najeriya takanas ya yi maraba da su a fadarsa ta Aso Rock don tattauna buƙatunsu ga gwamnati.

Kafin wannan ganawa ta maryacen Laraba, ‘yan ƙwadagon suna ganawa ne da kwamitocin da ya naɗa don tattaunawa da cimma yarjejeniya.

Nan gaba a ranar Alhamis ne, ‘yan ƙwadagon za su yi taro a tsakaninsu, inda Joe Ajero da Festus Osifo za su bayyana musu abubuwan da suka cimma a tattaunawarsu da Shugaba Tinubu, kafin su fitar da matsayar da suka ɗauka.

Rahotanni dai sun ambato su suna cewa Tinubu a yayin ganawar tasu, ya yi alƙawurra kan wasu buƙatu da suke fafutuka a kai.

Sanarwar da shugaban NLC Kwamared Joe da Festus Osifo na TUC suka fitar bayan ganawa da Tinubu ta ce shugaban ƙasar ya yi musu alƙawurra guda huɗu. Ga su kamar haka:

Tinubu ya yi alƙawarin cikin gaggawa zai sake fasali ga tsarin tattaunawar ɓangarorin biyu bisa doron shawarwarin da shugabannin ƙwadagon suka bayar.

Tinubu ya ba da tabbacin cewa matatar man fetur ta Fatakwal za ta fara tace mai nan da watan Disamban bana.

Tinubu ya ce zai tabbatar da ganin an cimma yarjejeniya cikin gaggawa a kan sabon albashin da za a riƙa biyan ma’aikatan Najeriya.

Tinubu zai ƙaddamar da tsari mafi sahihanci na iskar gas ɗin da zai iya maye gurbin man fetur a cikin makon gobe.

Majalisa

Wani muhimmin ci gaba da zanga-zangar ‘yan ƙwadago ta ranar Laraba ta samu, shi ne kai kokensu ga Majalisar Dattijai, daɗin daɗawa ma kuma ‘yan majalisar har suka fita suka saurare su.

Ko da yake, ana iya cewa matakin bai zo cikin sauƙi ba. Taƙaddama a kan shiga harabar majalisar ta janyo har an karya ƙofa, kafin masu zanga-zangar su yi kukan kura su kunna kai cikin farfajiyar ginin.

Daga bisani dai, mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Ali Ndume wanda Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya naɗa a matsayin wani kwamitin mutum uku da ya karɓi masu zanga-zangar, ya saurari kokensu.

Bayan sauraron nasu ne kuma, sai Sanata Ndume ya roƙe su, su dakatar da aniyarsu ta shiga yajin aiki washe gari ranar Alhamis, maimakon haka su bai wa dattijan mako ɗaya don ganin irin ƙoƙarin da za su iya wajen shiga tsakani da ɓangaren zartarwa.

Zanga-zangar ta gudana

‘Yan Najeriya da yawa na cike da shakku game da kiran da ƙungiyoyin ƙwadago suka yi na gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar ranar Laraba. A lokuta da dama, ƙungiyoyin ƙwadago kan janye irin wannan mataki da suka shirya ɗauka, sa’o’i ƙalilan kafin farawa.

Lokaci na baya-bayan nan da suka fasa ɗaukar irin wannan mataki shi ne ranar 19 ga watan Yuni, lokacin da kotun masana’antu ta ƙasa ta yanke hukuncin cewa umarnin da ta bayar tun ranar 5 ga watan, wanda ke hana ‘yan ƙwadago shiga yajin aiki yana nan daram.

Sai dai, ‘yan ƙwadagon sun yi nasarar taruwa a wuraren da suka tsara a cikin jihohin Najeriya, tare da gudanar da maci a kan tituna.

Barazanar sanya ƙafar wando ɗaya da masu yunƙurin kawo tarzoma kamar yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi kashedi ranar jajiberen zanga-zangar, bai razana ‘yan ƙwadago, ya sa su fasawa ba.

Zanga-zangar ta karaɗe ƙasa

Skip podcast promotion and continue reading

Korona: Ina Mafita?
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of podcast promotion

Zanga-zangar dai ta samu karɓuwa, inda aka gudanar da maci a manyan jihohin Najeriya. Ɗumbin ‘yan ƙwadago ne suka yi ado cikin tufafi masu launuka iri daban-daban tare da ɗaga tutoci da alluna da ƙyallaye masu rubuce-rubuce na saƙonni daban-daban da suke son isarwa.

An gudanar da tattaki a jihohi kamar Kano da Lagos da Kwara da Ogun da Kaduna da Ribas da Imo da Filato da Akwa Ibom kai har ma Abuja, babban birnin ƙasar.

A jihohi da dama, zanga-zangar ta haifar da tsaiko ga harkokin gwamnati da na tattalin arziƙi, yayin da aka ga raguwar ababen hawa a titunan manyan birane.

Akasari dai, an buɗe ofisoshin gwamnati, amma ba lallai ne ayyuka sun gudana kamar yadda aka saba ba.

Rahotanni da yammacin Laraba, sun ambato cewa gwamnati ta garzaya kotu, inda ta gurfanar da jagororin zanga-zangar bisa tuhumar raina kotu

Sanarwar da ‘yan ƙwadagon suka fitar bayan zanga-zangar ta ce duk da razanarwa da yankan baya, don sanyaya gwiwar ‘yan Najeriya a kan kada su shiga macin, amma dai matakin ya samu nasara.

Sanarwar ta ja hankali da cewa ‘yan ƙwadagon sun samu sammaci, a kan tuhumar da ake yi musu. Amma ko ma dai mene ne, ana iya cewa bakin alƙalami ya riga bushe game da zanga-zangar.

‘Yan ƙwadago sun yi amo

Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun ce sun kira zanga-zangar ne a faɗin ƙasa a matsayin wata kafa da ‘yan ƙasa za su bayyana fushinsu a kan manufofin gwamnati da ta kira “na durƙusar da talaka da kassara al’umma”.

Sun ce zanga-zangar ta aika wata alama mai ƙarfi da amo kuma a fayyace ga gwamnatoci a matakan tarayya da na jihohi cewa jama’a su ne sama da kowa kuma su ne mizani.

NLC da TUC sun dai yaba wa majalisar dokoki ta tarayya saboda sauraren abin da ta ce koke al’umma da kuma alƙawarin da ta yi da nuna tsananin fahimta a kan buƙatar gwamnati ta samar da mafita cikin hanzari kuma cikin taƙaitaccen lokaci don sassauta tsananin da tsadar farashin man fetur ya haddasa.

Sai nan gaba ne dai za a iya fahimtar ko amon da ‘yan ƙwadagon suka yi, ya shiga kan mahukunta ta kunnen basira, bisa la’akari da ganin matakan da za su bijiro da su don magance ɗumbin matsalolin da ke addabar talakawan ƙasar. Waɗanda har suke ingiza ma’aikata shiga yajin aiki da kuma fantsama kan tituna suna zanga-zanga.