Labarai

Sojojin Najeriya za su kwashe wasu bama-bamai da ba su fashe ba a Lagos

Sojojin Najeriya za su kwashe wasu bama-bamai da ba su fashe ba a Lagos

Hukumomin sojin Najeriya sun ce za a kwashe wasu bama-bamai da basu fashe ba bayan sun gano su a wurin da fashewar bam ta tashi bisa kuskure a Ikeja, sama da shekaru 21, dasuka gabata.

 

Fashewar wadda ta faru a ranar 27 ga watan Janairun 2002, a sansanin soji da ke Ikeja, ana kyautata zaton ta kashe aƙalla mutane 1,100 tare da raba sama da mutum 20,000 da muhallansu tare da jikkata wasu da dama.