Labarai

Sojoji sun kuɓutar Da wasu ɗalibai Da aka sace

Sojoji sun kuɓutar Da wasu ɗalibai Da aka sace

Sojojin Najeriya ƙarƙashin rundunar Hadarin Daji mai yaƙi da ‘yan fashin daji a arewacin Najeriya ta ce ta samu nasarar kuɓutar da wasu ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, da ‘yan bindiga suka sace da da tsakar daren ranar Asabar 14 ga watan Octoba.

 

‘Yan bindigar sun far wa ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Sabon Gida, da ke yankin Damba a karamar hukumar Gusau, cikin dare a lokacin da daliban suka fara bacci.

 

Inda suka fara harbin kan mai tsautsayi, lamarin da ya sa suka yi garkuwa da ɗaliban.

 

Cikin wata sanarwar da Rundunar hadarin Daji ta fitar – mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Kaftin Ibrahim Yahaya – ta ce rundunar ta samu nasarar kuɓutar da ɗaliban ne bayan da suka mayar da martani a kan lokaci yayin da aka sanar da su halin da ake ciki game da satar ɗaliban.

 

Sanarwar ta ce nan take rundunar haɗa kan dakarunta, inda suka datse hanyar da suke tunanin ‘yan bindigar za su ɓullo, inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar.

 

“Matsin da ‘yan bindigar suka sha ya tilasta musu tserewa tare da barin ɗaliban”, in ji sanarwar.

 

A lokacin musayar wutar- wadda aka yi da misalin ƙarfe12 na dare, dalibai biyu sun samu guduwa da kansu, yayin da jami’an tsaro suka ceto biyu.

 

A baya- bayan nan ‘yan bindiga sun ɓullo da salon kai wa ɗaliban jami’o’i hari tare da sace su a ɗakunan kwanansu.

 

Ko a watan Satumba ma sai da ‘yan bindigar suka kai wa ɗaliban na FUGUS hari a ɗakunan kwanansu inda suka sace ɗalibai masu yawa, wani lamari da ya tayar da ƙura a ƙasar.