Labarai

Sojoji Sun Kashe Mayakan ISWAP 6 A Borno

Sojoji Sun Kashe Mayakan ISWAP 6 A Borno

Sojoji Sun Kashe Mayakan ISWAP 6 A Borno

Sojojin Najeriya sun kashe mayakan ISWAP shida tare da fatattakar wasu da dama a wani harin kwantan bauna da kungiyar ta kai musu suna tsaksa…

Dakarun sojin Najeriya sun kashe mayakan ISWAP shida tare da fatattakar wasu da dama a wani harin kwantan bauna da kungiyar ta kai musu suna sintiri a unguwar Binduldul da ke kan hanyar Maiduguri-Gubio-Kareto-Damasak.

Sojojin da aka girke a Damasak sun yi musayar wuta da ’yan ta’addan suka tsere cikin daji, kamar yadda wata majiyar leken asiri ta shaida wa Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi.

 

Majiyar ta kara da cewa, sojojin sun shiga cikin dajin domin fatattakar ’yan ta’addar, kuma a yayin arangamar mayakan ISWAP da ba a tantance adadinsu ba sun samu raunuka.

Sojoji 3 ne suka samu raunuka a yayin arangamar, yayin da aka kwato bindigogin PKT guda biyu, AK-47 guda biyar, da motar bus kirar Hummer guda daya da ’yan ta’addar ke amfani da su.