Labarai

Shugaba Buhari bai yi nadamar Abinda Yayi ba

Tsohon shugaban Najeriya, Shugaba Buhari ya bayyana damuwa game da wani labari da ake ta yayatawa, inda aka ruwaito, tsohon mai ba shi shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Mista Femi Adeshina wai yana cewa Buharin yana nadamar wasu abubuwan da ya yi a lokacin mulkinsa na shekara takwas.

Mai magana da yawun tsohon shugaban, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa, an yi wa bayanan na Mista Femi Adeshina gurguwar fahimta ko kuma an sa son zuciya wajen fassara abin da ya fada.

A dangane da hakan ne Garba Shehu ya ce ba a yi wa Femi Adesina adalci ba.

Kakakin ya ce, “ita wannan jarida da ta ɗauki kanun labaran ta buga so suke su jawo hankalin mutane su sai da jaridarsu in ba don haka ba me aka yi na aikin da-na-sani?”

Ya ce abin da tsohon shugaban ya yi a lokacin mulkin nasa na kalamai da ayyuka jama’a aka yi wa domin amfanin ƙasar ba son-rai ba saboda haka maganar da-na-sani ba ta ma taso ba a kan haka.

“Duk abin da zai yi iya ƙarfinsa da jinin jikinsa ya yi don ya kyautata ƙasar Najeriya don ya kyautata rayuwa ta al’ummar Najeriya,” ya ce.

Ya ce akwai ayyuka da dama a fanni daban-daban da shugaban ya yi ana gani.

Ya koka da cewa, “Amma dama ƙasar haka ta gada idan giwa ta faɗi aka ce ai kowa ma wuƙarsa zai zaro ya ce bari ya zo ya yanka.”

“Amma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi rawar-gani kuma idan ba a faɗa yau ba nan gaba wataƙila wasu za su zo bayanmu su duba su yi mana adalci su ce ga abin da ya yi na alheri a ƙasar nan,” in ji kakakin.

Martani kan zargin jefa ƙasa cikin matsaloli

Dangane ya yadda ake zargin cewa gwamnatin Buharin ita ce sanadin halin da ƙasar take ciki a yanzu na wasu katutun matsaloli sai kakakin ya ce, ai daman a duk duniya babu wata gwamnati daya da za ta iya magance matsalolin ƙasa gaba ɗaya sai dai ta yi iya ƙokarinta ta tafi wata ta zo ta ɗora a ciyar da ƙasar gaba.

Ya ce, “Idan har an samu takura ko wani matsatsi dubawa za a yi a ga shin mene ne ya kawo wannan matsala.”

“Ba a taɓa samun wata gwamnati a ƙasar nan da ta samu kanta a karayar tattalin arziƙi irin lokacin Shugaba Muhammadu Buhari ba sabili da dogaro da muke yi da man fetur ya karye a duniya cutar Korona ta zo kowa ce ƙasa ta garƙame ƙofarta ta rufe tattalin arziƙi ya sake nutsewa,” in j shi

“Amma Alhamdulillahi sai da ya cicciɓo tattalin arziƙin Najeriya aka fitar da shi daga cikin wannan mawuyacin hali,” a cewar kakakin.

Garba Shehu ya ce suna alfahari da cewa babu wani sashe na Najeriya da ba za a ga wasu ayyuka na cigaban ƙasa da gwamnatin Buhari ta yi ba.

Ya ce, “muhimman ayyuka na raya ƙasa da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya yi don kyautata wa al’umma ai kamar ruwan sama ne in ma bai buge ka a gona ba zai buge ka a gida.”

Martani kan ƙin sauraren jama’a

Har wa yau danagane da batun Garba Shehun ya kuma yi suka ga fashin baki da aka yi da ya biyo bayan rahoton cewa Buharin ya yi nadamar wasu abubuwan da ya yi a lokacin mulkin nasa.

Ya ce: “Aka nemi wani ƙwararre wanda farfesa ne na siyasa wanda ya zo ya yi wani fashin baƙi wanda shi ma muke gani bai yi adalci ga Shugaba Muhammadu Buhari ba.”

“Ka ce wai Muhammadu Buhari ya yi mulkin dumukuraɗiyya ya kawo soja a ciki ya rufe ƙofa bai sauraron jama’a wannan ba haka yake ba.

Kuma shi kansa wannan bawan-Allah da ya faɗi waɗannan kalamai idan ƙofar ganin Buhari a rufe take ya akai shi ya ga Shugaba Muhammadu Buhari gida da ofis? Sai ya yi wa mutane bayani.” in ji shi.