
Mahukunta Nijeriya sun saki fasfo ɗin Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Daga Fatima Nuraddeen Dutsin-ma.
“A wani rahoto dake Bayyana mana yanzu haka cewa mahukunta Nijeriya sun saki fasfo Jagoran Harkan Musulunci a Nijeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta saki fasfo ɗin jagoran Harkar Musulunci da aka fi sani da ‘yan Shi’a
Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda sanadiyar riƙe fasfo ɗin nasa yasa bai bar Nijeriya ba domin fita ƙasar waje neman lafiyasa tun bayan sakinsa da wanke shi da kotu ta yi da shi da mai ɗakinsa shekaru 2 da suka gabata.”