Labarai

Rundunar Tsaron Najeriya Ta Ce Sun Hallaka Kimanin ‘Yan Ta’adda 50 A Jihar Imo

Rundunar Tsaron Najeriya Ta Ce Sun Hallaka Kimanin ‘Yan Ta'adda 50 A Jihar Imo

Rundunar tsaron kasar ta ce sun kuma cafke karin wasu ‘yan ta’adda guda dari da goma sha hudu.

 

ABUJA, NIGERIA – Daraktan cibiyar samar da bayanai na irin arangamar da dakarun kasar ke yi, Manjo janar Edward Buba ke bayyana hakan yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a hedikwatar tsaron kasar da ke Abuja.

 

Janaral Buba ya kuma nuna wa manema labarai wani faifan video mai tada hankali na wani daji mai suna Aku da ke yankin karamar hukumar Okigwe a jihar Imo da kuma ke zama sansani ko maboyar ‘yan awaren kudu maso gabas da ke rajin ballewa daga Najeriya.

 

Wannan wuri da kuma ke zama wurin yin tsafi na ‘yan ta’addan an nuno wata makara da wasu alamu na tsafi da ma kwarangwal da kan mutane.

 

Daraktan ya ce akwai da dama daga cikin faya fayen bidiyon da ba zai iya nunawa manema labarai ba saboda tsananin tashin hankalin da ke cikinsu inda su ke dauke da yadda ‘yan ta’addar ke daddatsa mutane gunduwa-gunduwa, su ke kuma cin naman mutane, abin da ya ce tuni sun rugurguza wurin.

 

Janar Edward Buba ya ce dakarun sun kuma yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan yankin Niger Delta inda suka rusa haramtattun matatun mai da jiragen ruwa da kuma wuraren adana man sata.

 

Tuni kuma babban hafsan rundunar tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirinsu na kara zage damtse wajen kara daukar matakai na inganta tsaro a kasar.

 

Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina: