Labarai

Rikicin Haiti ba matsalar Kenya ba ce – Odinga

Jagoran ‘yan adawar Kenya Raila Odinga ya nuna shakku kan matakin da kasar ta dauka na jagorantar rundunar tabbatar da zaman lafiya a kasar Haiti domin yaki da tashe-tashen hankula a can, yana mai bayyana matakin da cewa ba daidai ba ne.

Odinga, a wata hira da ya yi da wani gidan talbijin na kasar ranar Alhamis, ya ce shirin tura ‘yan sandan Kenya zuwa Haiti ba shi ne abin da ya kamata Kenya ta sanya a gaba ba. Ya kara da cewa tuni yankin gabashin Afirka yake fama da nasu “dumbin matsaloli”.

“Kafin ma ku zo Afirka, Haiti tana bakin kofar Amurka wadda ita ce kasa mafi karfi a duniya. Me ya sa za a dora wa Kenya alhakin jagorantar rundunar kasashen duniya a Haiti?”

Odinga ya ce halin da ake ciki a Haiti yana da hatsari, inda ya yi gargadin cewa shirin tura jami’an tsaron zai jefa rayukan ‘yan sandan Kenya cikin hatsari.

“Lokacin da akwatunan gawawwaki suka fara isowa nan, a lokacin ne za mu yi nadama. Haiti na da hatsari kuma akwai yiwuwar ‘yan sandanmu su fuskanci matsaloli a can,” in ji shi.

“Matsalar Haiti ta siyasa ce, ba wai bindiga take bukata ba, tana bukatar tattaunawa ne.” Odinga ya kara da cewa.

A ranar Litinin ne kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da tura dakarun kasashen duniya na tsawon shekara guda tare da yin nazari kan matsayinsu a kasar bayan wata tara.

Shugaban Kenya, William Ruto ya yi alkawarin cewa “ba za su bai wa al’ummar Haiti, kunya ba”.

Sai dai kuma wasu masu sukar lamirin matakin sun nuna rashin amincewarsu da shirin, inda suke nuna shakku kan yadda ‘yan sandan Kenya za su iya fuskantar gungu-gungun ‘yan bindiga a Haiti.