Labarai

Real Madrid ta koma jan ragamar teburin La Liga

Real Madrid ta koma jan ragamar teburin La Liga

Real Madrid ta koma jan ragamar teburin La Liga

Real Madrid

Real Madrid ta doke Girona 3-0 a wasan mako na takwas a La Liga da suka fafata ranar Asabar.

Real ta ci kwallon farko a minti na 17 da fara tamaula ta hannun Joselu, bayan da Jude Bellingham ya bashi kwallon, daga baya Aurelien Tchouameni ya kara na biyu.

Bellingham ne ya ci na ukun bayan da suka koma zagaye na biyu, kuma na bakwai da ya ci a raga tun bayan da ya koma Real a bana daga Borrusia Dortmund.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta daya ta hau kan saman Girona da Barcelona, wadda ta yi nasara a kan Sevilla ranar Juma’a.

Real din mai maki 21 tana ta daya a kan teburin La Liga, sai Barcelona ta biyu mai maki 20 da kuma Girona ta uku da maki 19.

Ranar Talata kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta ziyarci Napoli a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League.