Labarai

Najeriya na neman dala miliyan 400 daga Bankin Duniya don raba wa ‘yan kasar

Najeriya na neman dala miliyan 400 daga Bankin Duniya don raba wa 'yan kasar

Rahotanni sun ce gwamnatin Najeriya ta nemi karin rancen kudi na dala miliyan 400 daga bankin duniya, domin tallafa wa iyalai akalla miliyan 15 a fadin kasar, matakin da ta ce yana daga cikin jerin wadanda take dauka don ragewa marasa karfi radadin cire tallafin man fetur da ta yi.

Afrika
Najeriya
Nijar
Yankin – Hausawa
Turai
Asiya
Duniya
Koma shafin farko / Najeriya
Najeriya na neman dala miliyan 400 daga Bankin Duniya don raba wa ‘yan kasar
Rahotanni sun ce gwamnatin Najeriya ta nemi karin rancen kudi na dala miliyan 400 daga bankin duniya, domin tallafa wa iyalai akalla miliyan 15 a fadin kasar, matakin da ta ce yana daga cikin jerin wadanda take dauka don ragewa marasa karfi radadin cire tallafin man fetur da ta yi.

Wallafawa ranar: 15/10/2023 – 10:13

Minti 1

Nairar Najeriya da dalar Amurka REUTERS – AFOLABI SOTUNDE
Da:
Nura Ado Sulaiman
TALLA
Karin rancen na Dala miliyan 400 da Najeriyar ta nema dai zai sanya jimillar bashin da ta karba daga bakin duniyar kai wa Dala biliyan 1 da miliyan 200, la’akari da cewar a baya bayan nan bankin ya amince da ba ta Dalar miliyan 800, wanda su ma ta ce za ta raba wa marasa karfi, don saukaka musu matsin tattalin arzikin da suka shiga.

A ranar 1 ga watan Oktaba, yayin jawabi kan murnar zagayowar ranar da Najeriya ta samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka, shugaba Bola Tinubu ya sanar da shirin raba wa gidaje miliyan 15 kudi ta hanyar aike musu da tallafin ta asusunsu na banki, domin saukaka musu hauhawar farashin kayayyakin da suke fuskanta, saboda cire tallafin man fetur.

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa daga wannan wata na Oktoba, gwamnati za ta fara biyan Naira 25,000 ga iyalai miliyan 15, wadanda za su shafe tsawon watanni uku suna karbar tallafin.