Labarai

Messi zai koma tsohuwar kungiyarsa

Messi zai koma tsohuwar kungiyarsa

Alamu na kara nuna cewa dan wasan Ingila Jadon Sancho zai iya barin Manchester United a kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu, kuma tuni Borussia Dortmund ta nuna sha’awar lallabawa don dawo da kayanta (Sky Germany)

 

Dan wasan bayan Everton da Ingila na ‘yan kasa da shekara 21 Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, yana cikin jerin ‘yan wasan da United ke zawarci a kasuwar musayar ‘yan wasa ta gaba. (Mail)

 

Kofar Frank Lampard a bude take don tattaunawa da Rangers game da karbar ragamar kungiyar da ke neman maye gurbin tsohon kocinta Michael Beale. (Telegraph)

 

Shahararren dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 36, ya yanke shawarar komawa kulob dinsa na farko, Newell’s Old Boys, idan kwantiraginsa da Inter Miami ya kare a shekarar 2025. (Mirror).

 

Leeds, da Leicester da Burnley sun rubuta wasikar hadin gwiwa zuwa ga wadanda ake tunanin za su zama sabbin masu mallakar Everton, 777 Partners, cewa suna da niyyar gurfanar da kungiyar don neman diyyar fan miliyan 300 idan aka same su da laifin karya dokar kashe kudi a gasar Premier. (Mail)

 

Chelsea ce ke kan gaba wajen sayen dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 24, daga Napoli a bazara mai zuwa, yayin da Evan Ferguson na Brighton, mai shekara 18, da Ivan Toney na Brentford, mai shekara 27, suma ke cikin wadanda za su nuna sha’awarsu ta daukar dan wasan. (Caught Offside)

 

Rahotanni sun ce Barcelona za ta saurari tayin da ake yi wa manyan ‘yan was an da take amfanin da su yau da kullum, saboda har yanzu kulob din yana kasha sama da Yuro miliyan 270 da aka kayyade a gasar La Liga. (Sport Spanish)

 

Dan wasan tsakiya na Croatia, Luka Modric, wanda ake alakanta shi da komawa Inter Miami, zai iya barin Real Madrid yayin da kulob din na Sipaniya ke ganin dan wasan mai shekaru 38 ba ya taka leda yadda ya kamata. (Football Espana)

 

Dan wasan baya na Bayer Leverkusen dan kasar Holland Jeremie Frimpong, mai shekara 22, na shirin kulla sabuwar yarjejeniya da kulob din na Jamus, inda hakan zai kara darajar dan wasan da ke jan hankalin Manchester United da Real Madrid. (Daily Record)