Labarai

Me ya ingiza tubabbun Boko Haram gudanar da zanga-zanga?

Me ya ingiza tubabbun Boko Haram gudanar da zanga-zanga?

Gwamnatin jihar Borno ta yi ƙarin haske a kan zanga-zangar da tubabbun Boko Haram suka yi a wani sansanin sake tsugunnar da su.

Da yammacin Jumar nan ne tsoffin ‘yan ta-da-ƙayar-bayan suka ɗunguma kan titi a wajen birnin Maiduguri.

Rahotanni sun ce tubabbun Boko Haram ɗin sun fusata ne, inda suka fita wajen sansani tare da hawa kan titi suna zanga-zanga don nuna rashin jin daɗinsu a kan abin da suka kira gazawar hukumomi na cika alƙawurran da aka ɗaukar musu, bayan sun rungumi zaman lafiya tare da ajiye makamai.

Dubun dubatar mayaƙa da iyalan ‘ya’yan ƙungiyar Boko Haram ne suka ajiye makamai tare da miƙa wuya ga hukumomin Najeriya a baya-bayan nan.

 

Gwamnatin jihar Borno dai ta ce yayin da ƙura ta lafa, jami’an gwamnati daga bisani sun ci gaba da aikin ɗaukar bayanan tubabbun Boko Haram ɗin a kwamfuta.

 

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin tsaron cikin gida, Farfesa Usman A. Tar ya fitar, na cewa jimillar tubabbun Boko Haram 6,900 ne aka tantance su a ƙarƙashin wani shirin haɗakar hukumomi na ajiye makamai da kwance ɗamara da sauke kangarewa da sake tsugunnarwa da sulhuntawa da kuma mayar da su cikin jama’a.

 

Shaidu sun ce an tura sojoji, waɗanda suka datse masu zanga-zangar don hana su fantsama cikin gari.

 

Wani shaida daga Maiduguri da ya je wurin da tubabbun na Boko Haram suka yi zanga-zangar a gaban sansaninsu da ke wajen babban birnin, ya faɗa wa BBC cewa tsoffin mayaƙan sun fito da yawa, inda suke ta ihu da sowa a lokacin da suke bayyana koke-kokensu.

 

Ya ambato suna cewa, su ba su fita zanga-zanga don ɓarnata dukiyar kowa ba, amma dai suna magana da babban amo don kukansu ya isa kunnen mahukunta.

 

Sanarwar ta ce giɓin sadarwa da aka samu ne game da rukunin da ya kamata ya bayyana don ɗaukar bayanansu a wata rana da aka sanya a nan gaba, amma sai suka zo a ranar Juma’ar nan.

Lamarin da a cewar, gwamnatin Borno ya haddasa hargitsi a sansanin da ake aikin.

Gwamnatin jihar Borno dai ta ce an tsara gudanar da aikin ɗaukar bayanan tubabbun Boko Haram ɗin ne a kwamfuta, cikin rukuni shida wanda wani ayarin jami’in sirri da ƙwararru a fannin fasahar sadarwa da ke da matuƙar gogewa da tsare sirri cikin harkar tattara bayanai.

Sai dai ta ce daga bisani hukumomi sun yi nasarar shawo kan lamarin.

Me ya janyo zanga-zangar?
Skip podcast promotion and continue reading

Korona: Ina Mafita?
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi
End of podcast promotion
Rahotanni dai sun ce sojoji sun killace masu zanga-zangar don ganin ba su fantsama zuwa cikin garin Maiduguri ba. Sai dai tubabbun Boko Haram ɗin sun riƙa ɗaga murya a lokacin da suke magana akasari cikin harshen Kanuri.

An jiyo masu zanga-zangar na bayyana cewa cikin abubuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya har da batun kuɗin alawus na wata-wata wanda suka ce hukumomi sun gaza fara biyansu kamar yadda aka yi musu alƙawari.

Kuɗin dai shi ne zai ba su damar ci gaba da gudanar da sana’o’in da aka koya musu a sansanin, da kuma riƙe kawunansu hatta a lokacin da suka koma cikin al’umma.

Haka zalika, tubabbun Boko Haram ɗin sun koka a kan ƙarancin kulawar da suka ce suna samu a sansanin na birnin Maiduguri. Suna cewa abincin da ake ba su a sansanin ma ba ya isar su.

Sun nunar da cewa shi kasan zaman sansanin abu ne mai sa gundura, saboda turke su tsawon lokaci a wuri ɗaya.

Dangane da aikin ɗaukar bayanansu tantance su a kwamfuta, sun zargi hukumomi da fifita wasu, waɗanda akasari ba sa zaune a sansanin