Labarai

Matashi Ya Yi Wa ’Yar Shekara 62 Fyade A Borno 

Matashi Ya Yi Wa ’Yar Shekara 62 Fyade A Borno 

Matashi Ya Yi Wa ’Yar Shekara 62 Fyade A Borno

Dubun wani matashi mai shekara 37 ta cika bayan da ya yi wa wata tsohuwa ’yar shekara 62 fyade a Jihar Borno.

Dubun wani matashi mai shekara 37 ta cika bayan da ya yi wa wata tsohuwa ’yar shekara 62 fyade a Jihar Borno.

Matashin wanda yanzu haka yake komar ’yan sanda ya kuma sace wa dattijuwar kudi, bayan da ya yi mata fyaden a kauyen Panshani, gundumar Gasi da ke Karamar Hukumar Shani ta jihar.

An kama wanda ake zargin ne bayan dan uwan dattijuwar ya kai kara wurin ’yan sanda cewa tsohuwar mai shekara 62 na komawa gida daga unguwa ne matashin tsayar tare ta a hanya “ya yi mata fyade, ya kwashi kudi Naira dubu arba’in da biyu da dari bakwai a aljihunta.

“Don haka yanzu haka ana ciga da bincike, kuma da zarar an kammala za a mika shi gaban kuliya don fuskantar hukuncin da ya yi dai-dai da shi,” in ji Kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammad Yusufu.

Ya kara da cewa a cikin watanni ukun da suka gabata rundunar ta kama mutane akalla 500 kan aikata laifuka daban-daban a sassan jihar, kuma yawancinsu an mika su gaban kuliya.