Labarai

Matar Da Aka Kama Da Magazine Na Harsashen Bindiga Guda Biyu A Jihar Katsina.

Ƙarin Bayani Dangane Da Matar Da Aka Kama Da Magazine Na Harsashen Bindiga Guda Biyu A Jihar Katsina

 

Daga Muhammad Aminu Kabir

 

Bisa ga bayanai da muka samu Ita wannan baiwar Allah Matar Soja ce ta baro Bauchi ne saboda sun samu Hatsaniya da shi Sojan sai ta ɗauki Jakarsa ta zuba kayanta a ciki ta kamo hanya ta baro masa ƴayan su ba tare da ya sani ba, kuma a rashin Sa’a tabar wayarta a gida ba tare da tasan wayar bata jikinta ba saida tazo Katsina An ajeta a tasha kuma a Lokacin ana binciken kowaye yazo tasha zai shiga mota ne ko zai hau sai an bincikeshi.

 

Shine ana duba kayanta a ka ga waɗannan 2 Magazine ɗin kuma ita bata san dasu ba saida aka nuna mata aka tambaye ta wannan pa tace bata san dasu ba aka garzaya wurin ƴan Sanda don faɗaɗa bincike nan aka san cewa Wurin yayarta tazo a nan Katsina aka tambaye ta wayarta a nan ne tasan tabaro wayar a Bauchi, sai ta faɗi unguwar da Aunty ta take da kuma sunanta akaje aka faɗawa Aunty ta tazo wurin.

 

A kayi bincike sosai, sai case ɗin ya koma wurin Sojojin Katsina Saboda Ita Aunty ta, ta kira mijin Yarinyar ta faɗa masa shi kuma dole yaje yakai report a don yasan da waɗannan bullets ɗin a cikin jakar, shine aka kira Sojojin Katsina suka anshi case ɗin.

 

Kawo yanzu dai Mijin nata yana tsare Saboda sakacin da yayi na barin Harsasai a gidan har hakan tafaru Allah ya kyauta gaba ya bashi mahita Amin.

 

Muna ƙara Addua duk wanda yake da sa hannun wajen hana Al’umma zaman lahiya Allah ya kama shi kowanene, Allah ya san su mu bamu sansu ba muna roƙon Allah ya tona masu Asiri Allah ya kamasu irin kamun shi Alfarmar Sayyadina Rasullullahi Sallallahu Ta’alah Alaihi Wasallam Amin.

 

Allah ya ƙara zaunar da ƙasar mu lafiya. Amin.