Makaho Ya Damfari wata Mata million 19 Kuma Yayi zina Da ‘yar ta
Makaho Ya Damfari wata Mata million 19 Kuma Yayi zina Da 'yar ta

Makaho Mai Maganin Gargajiya Ya Damfari Dattijuwa Naira Miliyan 19, Ya Kuma Kwanta Da Ƴarta, Jikar Ta
Makaho Mai Maganin Gargajiya Ya Damfari Dattijuwa Naira Miliyan 19, ya kuma kwanta da ƴarta, jikar ta
Wani makaho mai maganin gargajiya mai suna Owolabi Adefemi wanda aka fi sani da Ojunu ya damfari wata tsohuwa Naira miliyan 19.
Jaridar Legit Hausa ta ruwaito tsohuwar da aka damfara mai suna Madam Alimot ta kawo ‘yar ta ne don ya warkar da ita.
A cewarta, ta rasa dukkan ‘ya’yanta 15 inda su ke rasuwa amma yanzu saura guda uku kacal shi ne ta zo neman taimako wurinshi.
Makahon mai maganin ya umarci matar ta kawo saniya don a sadaukar da ita saboda iftila’in da ya sauka a gidanta.
Matar ta yi kokarin samar da kudaden da ake bukata, daga nan ne ya rin ka neman karin kudade don yin aiki, kafin wani lokaci ya karbi ya kai miliyan 19 wanda sai da ta siyar da gidajenta biyu.
Wanda ake zargin har ila yau ya kwanta da diyar matar da kuma jikarta a wasu lokuta.