Labarai

Kungiyar Kwadago Zata Tsamduma Yajin Aikin A Dukkanin Fadin Najeriya.

YAJIN AIKIN GAMA GARI: Kowa Ya Tanadi Abinci Sakamakon Yajin Aikin Gama-gari Da Za’a Shiga, Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Bawa ‘Yan Najeriya Shawara

 

YAKIN AIKIN KUNGIYAR KWADAGO

 

Shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, da takwarorinsu ta ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya, TUC, sun shawarci al’ummar Najeriya da su tanadi kayan abinci saboda yajin aikin da zasu fara a ranar talata 03 ga watan Oktoba.

 

A ranar Juma’a, shugabannin ƙungiyoyin biyu sun ƙi halartar taron da gwamnatin tarayya ta kira a ƙoƙarinta na daƙile yajin aikin da ake shirin yi a faɗin ƙasar daga ranar 3 ga watan Oktoba.

 

Yajin aikin da ake shirin yi a faɗin ƙasar, za a yi shi ne domin tilastawa gwamnati ta magance matsalolin da ‘yan Najeriya suka shiga, sakamakon cire tallafin man fetur da kuma nuna halin ko in kula da yanayin da ‘yan Najeriya suke ciki.

 

Ƙungiyoyin ƙwadagon guda biyu sun kuma shawarci ‘yan Najeriya da su tara kayan abinci domin yajin aikin zai sa a rufe duk wasu harkokin tattalin arziki a ƙasar.

 

A cewar ƙungiyoyin ƙwadagon biyu, gayyatar da gwamnati ta yi musu ta zo ne a makare, don sun bar Abuja babban birnin Najeriya domin gudanar da wasu aiyuka.

 

TSAKANIN GWAMNATI DA YAN KWADAGO 

 

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin ta kira taron gaggawa da shugabannin ƙungiyoyin NLC da TUC a ƙoƙarin da take yi na daƙile yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago da ƙawayenta ta ‘yan kasuwa suka shiga.

 

Rahotanni sun nuna cewa taron wanda aka shirya yi ranar Juma’a da karfe 12 na rana a ɗakin taro na ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa dake Villa, daga baya aka canza lokaci zuwa yamma, domin baiwa NLC da TUC damar zuwa wajen taron.

 

A cewar wata majiya, NLC da takwararta ta TUC sun samu goron gayyatar gwamnati da safiyar juma’a ta hannun ma’aikatar ƙwadago da samar da ayyukan yi.