
Al’ummar Paris, babban birnin Faransa da sauran biranen ƙasar na fama da matsalar kudin cizo yayin da ƙasar ke shirye-shiryen ɗaukar baƙuncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics.
Yanzu haka ana ganin irin waɗannan ƙwari a wurare da dama a biranen.
Sai dai lamarin ya samo asali ne tun daga shekarun da suka gabata.
Wani masani kan ƙwari, Jean-Michel Berenger ya ce “a ƙarshen lokacin zafi na kowace shekara akan samu ƙaruwar kuɗin-cizo.”
Ya ƙara da cewa “hakan na faruwa ne saboda mutane da ke yawan tafiye-tafiye a watannin Yuli da Agusta, kuma sukan kwaso su a cikin kayansu.”
Sai dai a cewarsa “yawan kuɗin-cizon da ake samu na ƙaruwa a kowace shekara.”
Yanzu haka dai gwamnatin shugaba Emmanuel Macron na buƙatar ganin an ɗauki mataki.