Labarai

Kotu Ta Dawo Wa Dan Majalisar NNPP Kujerarsa A Kano

Kotu Ta Dawo Wa Dan Majalisar NNPP Kujerarsa A Kano

Kotu Ta Dawo Wa Dan Majalisar NNPP Kujerarsa A Kano » Alfijir

Kotun Daukaka Kara ta dawo wa dan Majalisar Tarayya na jam’iyyar NNPP daga mazabar Tarauni a Jihar Kano, Mukhtar Umar Yarima, kujerarsa da kotun sauraron kararrakin zabe ta kwace.

A watan Agusta ne dai kotu ta soke nasarar dan majalisar sannan ta ayyana abokin takararsa na jam’iyyar APC, Hafizu Ibrahim Kawu, a matsayin zababben dan majalisar.

 

Kotun dai a wancan lokacin ta soke nasarar Yarima ne saboda ta ce sunan da ke jikin takardar shaidar kammala firamarensa da ya gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ba nashi ba ne.

Alkalan kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a I.P. Chima ce ta jagoranci yanke hukuncin.

To sai dai a yayin zamanta na ranar Asabar, Kotun Daukaka Karar ta ce kotun farko ta kasa fito da yadda dan majalisar ya gabatar da takardar da ba ta shi ba.