Labarai

Ko cin abinci sau uku a rana na da illa?

Ko cin abinci sau uku a rana na da illa?

Kana cin abinci sau uku a rana? Ana ƙara samun fitowar bayanai game da wannan tsarin cin abinci.

 

Ana fada mana cewa karin kumallo shi ne abincin da ya fi matuƙar muhimmanci a rana, akan bayar da hutun cin abincin rana a makarantu da wuraren aiki, sannan kuma a haɗu da iyalai domin cin abincin dare.

 

To amma hakan shi ne hanyar da ta fi dacewa ta cin abinci?

 

Kafin mu yi tunani game da yadda za mu ci abinci, masana kimiyya na shawartar mu da yin tunani kan hakan.

 

Akwai jita-jita da ake ta yaɗawa game da tsawon lokacin da ya kamata a ɗauka, tsakanin cin abinci, inda ake ganin ya kamata ya zama sa’o’i takwas.

 

Idan muka ɗauki sa’o’i 12 ba tare da cin abinci ba, ƙwayoyin narkar da abinci da ke cikin ‘yayan hanjinmu za su samu hutu, kamar yadda Emily Manougian ta cibiyar binciken halittu da California ta bayyana.

 

Farfesa Rosalyn Anderson ta jami’ar Wisconsin ta gudanar da bincike kan amfanin taƙaita sinadaran ‘Calories’ a jikin ɗan’adam, ta ce tsawon lokacin da ake ɗauka ba tare da cin abinci ba na taimaka wa jiki”.

 

“Daukar lokaci ba tare da cin abinci ba, kan taimaka wajen sanya jiki a mabambantan yanayi, ta yadda zai iya gano matsalolin da jikin ke fuskanta da kuma share gurɓatattun abincin da suka rage a jikin ɗan’adam”.

 

Farfesa Anderson ta yi iƙirarin cewa ɗaukar tsawon lokaci ba tare da cin abinci ba zai yi daidai da tsarin halittar jikinmu. Hakan zai bai wa jiki hutu ta yadda zai iya taskance sinadarai tare da tura su wuraren da ake buƙatarsu a jikin ɗan’adam.

 

Rashin abinci zai kuma taimaka wajen daidaita sinadarin glucose a cikin jini bayan cin abinci, kamar yadda Farfesa Antonio Paoli, masanin atisaye da wasanni a jami’ar Padua da ke Italiya.

 

Ya ƙara da cewa ƙaruwar sinadarin glucose a cikin jini zai sa mutum ya samu ƙarancin maiko a jikinsa.

 

Alƙaluman da muka samu sun nuna cewa cin abincin dare da wuri tare da ƙara tazarar lokacin tsakanin cin abinci zai taimaka wa jikinmu wajen magance wasu cutuka,” in ji Farfesa Paoli.

 

Amma idan tazarar lokaci tsakanin cin abinci na da muhimmanci, sau nawa ya kamata mu ci abinci a tsakanin sa’o’i takwas?

 

Wasu masana ciki har da Farfesa David Levitsky na jami’ar Cornell da ke New York, na ganin cewa zai fi kyau a riƙa cin abinci sau ɗaya a rana.

 

“Akwai hujjoji masu yawa, misali idan zan nuna maka abinci ko hotonsa za ka ji kamar za ka ci, ke nan sa rai da ci shi ke kawo yunwa kamar yadda Hausawa ke cewa”, in ji shi.

 

Ya kara da cewa a baya, lokacin da ba mu da firinji ko kantunan sayar da kaya, mukan ci abinci ne kawai a lokacin da muka same shi.

 

Serene Charrington-Hollins masaniyar tarihin abinci ta ce a tarihance akan ci abinci sau ɗaya ne a rana, wanda ake ci da rana.

 

To amma yunwa ba za ta yi mana illa ba idan sau ɗaya za mu riƙa cin abinci a rana?

 

Ba lallai ba ne, in ji Levitsky, saboda yunwa wani abu ne da ƙwaƙwalwa ke ji.

 

”Da safe za mu ji tamkar ana umartarmu da cin abinci, haka ma da tsakar rana, to amma hakan ba komai ba ne” in ji shi.

 

Ya ƙara da cewa alƙaluman sun nuna cewa idan ka tsallake karin kumallo za ka samu ƙarincin sinadaran ‘calories’ a wannan rana.

 

“An tsara rayuwarmu kan cin abinci da ɗaukar lokaci ba tare da ci ba”, kamar yadda masana suka bayyana, to sai dai Levitsky bai amince da wanna tsari ba musamman ga mutanen da ke da cutar ciwon suga.

 

A lokaci guda, Manougyan ba ta amince da batun cin abinci sau ɗaya a rana ba, saboda a ganin ta hakan zai ƙara haifar da ƙaruwar sinadaran glucose a cikin jini, ko kuma rashinsa gaba ɗaya.

 

Kuma rashin sinadarin glucose a cikin jini na tsawon lokaci, ka iya haifar da cutar ciwon suga nau’in ‘type 2’.

 

Manougyan ta ce rage sinadarin glucose a cikin jini na buƙatar cin abinci fiye da sau ɗaya a rana, ta yadda jikin ba zai fuskanci mummunar yunwa ba tare da sakin sinadaran glucose masu yawa idan an ci abinci.

 

A maimakon haka, ta ce yana da kyau a ci abinci sau biyu ko sau uku a rana domin samun wadatattun sinadaran ‘calories’ a jiki.

 

Domin kuwa cin abinci da tsakar dare na tattare da tarin matsalolin da za su iya haifar da wasu cutuka ciki har da ciwon suga da ciwon zuciya.

 

“Idan ka ci abincinka da wuri, jikinka zai samu damar narƙar da shi domin yin amfani da shi a wannan rana, a maimakon ajiye shi a matsayin maiƙo”, in ji Manougyan.

 

Haka kuma bai kamata a ci abinci da sassafe ba, domin a cewarta hakan ba zai ba ka damar daɗewa ba tare da cin abinci ba. Haka kuma cin abinci da zarar an tashi daga baccin safe ya saɓa wa al’adar jikinmu, kamar yadda masu binciken suka bayyana.

 

Idan dare ya yi jikinmu kan saki sinadarin melatonin domin taimaka wa ɗan’adam yin bacci, sinadarin melatonin kan dakatar da fitar sinadarin insulin da ke taskance glucose a jikin ɗan’adam.

 

Sakamakon sidanarin melatonin da jiki ke saki, jiki kan yi amfani da shi don tabbatar da cewa ba a samun sinadarin glucose masu yawa a lokacin da muke bacci ba, in ji Manougyan.

 

“Mutanen tsohuwar daular Girka ne suka fara ɓullo da karin kumallo, inda suke cin jiƙaƙƙen garin alkama da ruwan inabi, sai kuma su ci abinci marar nauyi da rana sannan abinci mai nauyi da dare”, in ji Charrington-Hollins.

 

Da farko masu mulki da dukiya ne ke iya yin karin kumallo, in ji ta.

 

Batun karin kumallo ya zama ruwan dare ne a ƙarni na 17, ga masu ido da kwalli a lokacin.

 

“Batun karin kumallo da ake da shi a yanzu ya samo asali ne a ƙarni na 19 zamanin samuwar masana’antu bayan da aka ɓullo da sa’o’in aiki”, in ji Charrington-Hollins.

 

Hakan ya sa aka ɓullo da cin abinci sau uku a rana.

 

Amma bayan yaƙin duniya na biyu a lokacin da abinci ya fara tsada, batun samun abin karin kumallo ya tsananta, lamarin da ya sa mutane da dama suka haƙura da shi.

 

“Aka daina batun cin abinci sau uku a rana”, in ji Charrington-Hollins. “A shekarun 1950 ne karin kumallo ya zama abin da muka sani a yau”, in ji ta.

 

Don haka a kimiyyance ake cewa ingantacciyar hanyar cin abinci ita ce cin abinci sau biyu ko sau uku a rana tare da jimawa ba tare da ɗaukar tsawon lokaci cikin dare ba tare da cin abinci ba.

 

Haka kuma aka hana cin abinci da tsakar dare da kuma farar safiya.

 

To amma hakan ya kamata?

 

Manougyan ta ce babu buƙatar yin magana kan lokacin da ya fi dacewa a ci abinci, saboda yana da wahala ga wasu mutanen su iya tsayawa a kan lokacin da aka kiyasta, musamman ga waɗanda ke aiki da daddare.

 

Faɗa wa mutanen kar su ci abinci bayan ƙarfe 7 na yamma ba daidai ba ne, saboda mutane na da mabambantan tare-taren lokutan aiki. Idan kana son bai wa jikinka hutun cin abinci da daddare, to kar ka ci abinci da tsakar dare, ko da sanyin safiya, sannan ka yi ƙoƙarin kauce wa cin abinci mai yawa a lokacin cin abincinka na ƙarshe a rana”, in ji ta.

 

Kan batun lokutan da ya kamata a ci abinci, Charrington-Hollins ta ce akwai buƙatar samar da sauye-sauye.

 

“Tsawon ƙarnuka mukan ci abinci sau uku a rana, amma a yanzu ana ƙalubalantar wannan tsari, kuma ɗabi’ar mutane game cin abinci na ci gaba da sauyawa, a yanzu muna samun lokutan hutu masu yawa, sannan ba ma yawan aikin da muke yi a ƙarni na 19, don haka ba mu buƙatar yawan sinadaran calorin”, in ji ta.