Labarai

Katsina Ta Kaddamar Da Dakarun Tsaron Al’umma 1,466

Katsina Ta Kaddamar Da Dakarun Tsaron Al’umma 1,466

Katsina Ta Kaddamar Da Dakarun Tsaron Al’umma 1,466

 

A yau Talata Gwamna Umar Dikko Radda ya jaogaranci kaddamar da jami’an tsaron na Community Watchcops su 1,466 daga fadin jihar.

Jihar Katsina ta kaddamar da rundunar jami’anta na sintiri domin tunkarar matsalar tsaro da ’yan ta’adda da ke ci wa tuwo a kwarya.A yau Talata Gwamna Umar Dikko Radda ya jaogaranci kaddamar da jami’an tsaron na Community Watch Corps su 1,466 daga fadin jihar.

 

An kaddamar da jami’an na Community Watchcops ne bayan da suka samu horo na tsawon watanni biyu karkashin shirin da gwamnan ya kawo.

An dai zabo matasan da aka horar ne daga yankunan da suke fama da wannan matsala.

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnonin jihohin Kano, Yobe, Zamfara, da Kebbi sun halarci taron yaye jamia’n tsaron.