Kamfanin Nokia na shirin sallamar ma’aikata kusan 14,000
Kamfanin Nokia na shirin sallamar ma'aikata kusan 14,000

Kamfanin Nokia na shirin sallamar ma’aikata kusan 14,000
Kamfanin wayoyin hannu na Nokia na shirin sallamar ma’aikatansa da adadinsu ya kama daga dubu 9 zuwa dubu 14.
Ofishin kamfanin Nokia da ke birnin Paris na kasar Faransa kenan. REUTERS – Benoit Tessier
Cikin sanarwar da kamfanin ya fitar ya ce zai kammala daukar matakin ne nan da zuwa karshen shekarar 2026 domin tsuke bakin aljihunsa, biyo bayan koma bayan kashi 20 cikin 100 na kudaden shigar da ya saba samu a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban shekarar nan.
Shugabannin kamfanin sun ce zuwa karshen shekarar ta 2026, suna sa ran alkinta rarar kudaden da suka kama daga euro miliyan 800 zuwa euro biliyan 1 da miliyan 200.
A halin yanzu, yawan ma’aikatan kamfanin na Nokia ya kai dubu 886 a sassan duniya, duk da rage dubban guraben ayyukan da ya rika yi tun daga shekarar 2015.